Ana Binciken Tsohon Shugaban Amurka Donald Trump, FBI Sun Lalube Gidansa

Ana Binciken Tsohon Shugaban Amurka Donald Trump, FBI Sun Lalube Gidansa

  • Ma’aikatar shari’a ta kasar Amurka tana binciken Donald Trump da zargin sabawa dokar sirri
  • Jami’an FBI sun dura gidan tsohon shugaban kasar, sun bincike dakuna domin samun bayanai
  • A karshe an tattaro akwatuna dauke da bayanan sirri da bai kamata kowa ya san da zamansu ba

Florida - Jami’an hukumar bincike na FBI ta gano akwatuna fiye da 20 masu alamar sirri na matakin farko a lokacin da suka lalube gidan Donald Trump.

Gidan yada labarai na Sky News ya kawo rahoto cewa takardun kotu suka tabbatar da haka.

An samu wadannan takardu masu dauke da bayanan sirri da suka shafi harkar tsaro a wani katafaren gidan tsohon shugaban na Amurka a birnin Florida.

Hukumar FBI ta tabbatar da cewa ana zargin Donald Trump da sabawa dokar sirri. Tattara bayanan asiri ko mika su ga wani laifi ne a dokar Amurka.

Kara karanta wannan

Abuja: An kame wasu mutane 480 da ake zargin sun tsere daga magarkamar Kuje

A wadannan akwatuna 20 da aka samu a gidan Trump, 11 daga cikin akwatunan na dauke da tulin bayanan sirri da bai dace su shiga hannun kowa ba.

An kuma samu hotuna da rubutu da kuma bayanai a kan ‘Shugaban kasar Faransa’, aka dauke su.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Donald Trump
Donald Trump a jirgi Hoto: www.nytimes.com
Asali: UGC

An lalube dakuna 53

Yayin da tsohon shugaban kasar yake kukan an auka masa gida, rahoton da aka fitar a ranar Juma’a yace jami’an na FBI sun fasa wani akwatin ajiyarsa.

Da yake magana a shafin sada zumunta na Truth –Trump yace kayan ba na sirri bane, kuma ya yi niyyar maida su, don haka babu dalilin shiga gidansa.

Jami’an na FBI sun lalube dakuna 58 da ban dakuna 33 a wannan gida mai girman eka 17. Sai da aka bincike duk wuraren ajiyan da ke gidan Trump.

Kara karanta wannan

Mutumin da aka daba wa wuka saboda batanci ga Annabi na can asibiti rai hannun rabbaba

Bayanan afuwar da aka yi wa Roger Stone suna cikin takardun da aka samu. Stone yana cikin wadanda suka zuga Trump ya yi takarar shugaban kasa.

Daga baya aka samu Stone da laifin tsoma baki a harkar zaben kasar Rasha da aka yi a 2016. A Disamban 2020 gwamnatin Trump ta yafe masa laifinsa.

VOA tace ma’aikatar shari’a ce take gudanar da binciken, amma ba a kai kara zuwa kotu ba.

Korafin Kiristocin Najeriya

Kun samu labari cewa nan gaba kadan CAN za ta fitar da jerin duka wasu makarantun gaba da sakandare da ake zargin ana muzgunawa Kiristoci.

Kungiyar CAN tace akwai wuraren da ake hana kiristoci damar gina coci inda suke yin ibada, alhali Musulmai sun gina masallatansu, suna bautar Allah.

Asali: Legit.ng

Online view pixel