Faloli 6 na azumin watan Ramalana

Faloli 6 na azumin watan Ramalana

- Ma’anar kalmar "Azumi" a larabci shi ne kamewa da barin wani abu

- Ma’anar Azumi a Shari’a shi ne bautawa Allah ta hanyar kamewa daga cin abinci da abin sha da jima’i, tun daga hudowar Al fijir har zuwa faduwar rana.

Azumi yana da falala mai girma, da lada mai yawa, ribi-ribi. Allah Madaukakin Sarki ya raba azumi zuwa gare shi, saboda girmama shi da daukaka shi.

Ya zo a cikin hadisin Qudusi daga Abu Hurairata – Allah ya yarda da shi – ya ce, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “Dukkan aikin Dan Adam ana ninka masa shi, ana ninka kyakkyawa sau goma, har zuwa ninki dari bakwai.

Allah Mai girma da buwaya ya ce, “Sai dai azumi, hakika shi nawa ne, ni ne nake ba da ladansa, mutum yana barin sha’awarsa da abincinsa saboda ni.

Mai azumi yana da farin cikin biyu, farin ciki yayin buda bakinsa, da farin ciki yayin haduwa da Ubangijinsa.

Warin bakin mai azumi ya fi almiski kamshi a wurin Allah” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].

Azumin Watan Ramadan

Azumin watan Ramadan rukuni ne daga cikin rukunan musulunci, kuma farilla ne da Allah ya farlanta a kan bayinsa.

Allah Madaukakin Sarki ya ce, “Ya ku wadanda suka yi imani an wajabta muku azumi kamar yadda aka wajabta wa wadanda suke gabaninku don ku samu taqawa”. (Suratul Baqarah: 183)

Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “An gina musulunci a bisa ginshikai biyar” [Buhkari ne ya ruwaito shi]. Sai ya ambaci “Azumin watan Ramadan” daga cikinsu.

Hikimar Shar’anta Azumi

1 – Tabbatar da tsoron Allah, wajen amsa wa umarninsa, da biyayya ga shari’arsa. Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “(An wajabta muku azumi ne) ko kwa samu tsoron Allah” (Suratul Baqara : 183).

2 – Saba wa kai haquri, da qarfafa wa zuciya wajen danne sha’awa.

3 – Saba wa mutum da kyautatawa, da jin tausayin mabukata da talakawa, saboda idan mutum ya dandani yunwa zuciyarsa za ta yi laushi ta karkata zuwa ga mabukata.

4 – Samun hutu a jiki da samun lafiya a cikin azumi.

Sharuddan Wajabcin Azumi

1 – Musulunci : Azumi ba ya wajaba a kan kafiri.

2 – Balaga : Azumi ba ya wajaba a kan yaro karami, sai dai za a umarce shi da yi idan zai iya, don ya saba.

3 – Hankali : Azumi ba ya wajaba a kan Mahaukaci.

4 – Samun Iko : Azumi ba ya wajaba a kan wanda ba zai iya yi ba kamar mace mai jini, mara lafiya ko matafiyi. (Amma akwai ramuwa a kansu).

Wasu Daga Cikin Falalolin Watan Ramadan

1 – A watan Ramadan ana bude kofofin Aljannah, ana rufe kofofin wuta, ana daure kangararrun shaidanu, zuciya tana fuskantar aikin alheri.

Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “Idan Ramadan ya zo, sai a bude kofofin sama, a rufe kofofin Jahannama, a daure Shaidanu”. [Buhkari ne ya rawaito shi]

2 – Yin azumi da tsayuwar sallar asham saboda Allah da neman lada yana gafarta abin da ya gabata na zunubai.

Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “Wanda ya yi azumin watan Ramadan, yana mai imani da neman lada, za a gafarta masa abin da ya gabata na zunubansa” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].

Ya sake cewa : “Wanda ya yi tsayuwar sallah a watan Ramadan, yana mai imani da neman lada, za a gafarta masa abin da ya gabata na zunubansa”. [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi]

3 – A cikin watan Ramadan akwai daren Lailatul Qadri, wanda Allah yake cewa a kansa “Daren lailatul Qadri ya fi wata dubu alheri”. (Suratul Qadr : 3)

Duk wanda ya tsaya a cikin wannan dare yana mai imani da Allah da neman lada to za a gafarta masa abin da ya gabata na zunubansa.

Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “Wanda ya tsaya a daren lailatul Qadri yana mai imani da Allah da neman lada to za a gafarta masa abin da ya gabata na zunubansa” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].

4 – Umara a cikin Ramadan tana daidai da yin aikin Hajji tare da Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ). Manzon Allah ya ce, “Umara a cikin Ramadan tana daidai da aikin hajji tare da ni” [Muslim ne ya rawaito shi].

5 – Watan Ramadan watan Al-Qur'ani ne, a cikinsa aka saukar da shi, don haka ya dace a yawaita karanta shi a cikin wannan wata.

Allah ya ce, “Watan Ramadan wanda aka saukar da Al- Qur'ani a cikinsa, shiriya ne ga mutane, da ayoyin bayanannu da rarrabe wa tsakanin karya da gaskiya” (Suratul Baqara : 185).

6 – Watan Ramadan wata ne na kyauta da ciyarwa da sadaka. An karbo daga Abdullahi dan Abbas – Allah ya yarda da shi – ya ce, “ Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya fi dukkan mutane kyauta, ya kasance lokacin da yafi kyauta shi ne a cikin Ramadan, lokacin da Mala'ika Jibrilu yake haduwa da shi.

Mala’ika Jibrilu yana haduwa da shi a kowane dare a cikin Ramadan, ya yi karatun Alqur'ani tare da shi. Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya fi kowa kyauta lokacin da Mala'ika Jibriru yake haxu da shi, ya fi iska sakakkiya kyauta”[Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel