Jerin kasashen da suke awanni 22 suna azumi

Jerin kasashen da suke awanni 22 suna azumi

- Watan Ramadana wata ne da al'ummar Musulmai suke yin azumi na tsawon kwana 29 zuwa 30 daga fitowar alfijir zuwa faduwar rana a kowacce shekara

- Amma tsawon sa'o'in azumin yana bambanta a wasu kasashen na duniya, inda sa'o'in wasu kasashen bai kai na wasu kasashen tsawo ba

Jerin kasashen da suke awanni 22 suna azumi
Jerin kasashen da suke awanni 22 suna azumi

Watan Ramadana wata ne da al'ummar Musulmai suke yin azumi na tsawon kwana 29 zuwa 30 daga fitowar alfijir zuwa faduwar rana a kowacce shekara. Amma tsawon sa'o'in azumin yana bambanta a wasu kasashen na duniya, inda sa'o'in wasu kasashen bai kai na wasu kasashen tsawo ba.

A yanayi na zafi, kasashen da suke arewacin duniya kamar irin su yankin Turai suna shafe yini mai tsawon gaske kafin su sha ruwa, a lokacin da wasu kasashen yankin Afirka kuma suke fuskantar matsanancin zafin rana.

To a wannan shekarar ma azumin a wasu kasashen na duniya ya bambanta da awanni 10 zuwa awanni 22.

Majiyar mu Legit.ng ta binciko muku yanda wasu kasashen duniya ke shafe awanni masu yawan gaske da azumi a bakin su.

DUBA WANNAN: Hanyoyi 5 da za abi domin samun ingantacciyar lafiya a Ramadan

Jerin kasashen duniya da awannin da suke yi da azumi a bakin su.

Kasar Greenland itace kasar da tafi kowacce kasa tsawon sa'o'in azumi. Sukan tsaya da yin sahur da karfe 2:00 na dare, sannan su sha ruwa da misalin karfe 12 na dare.

Kasar Iceland da kasar Rasha sukan daina sahur tun karfe 2 na dare, sannan su sha ruwa da misalin karfe 10 na dare.

Kasar Birtaniya suna shafe sa'o'i 19 basu sha ruwa ba.

Kasashen China, Faransa da kasar Kanada suna shafe sa'o'i 17 suna azumi.

Wasu yankuna na kasar Amurka sukan shafe sa'o'i 15, yayin da wasu yankunan kuma ke shafe sa'o'i 17.

Kasar Afghanistan sukan shafe sa'o'i 16 da azumi a bakin su.

Kasashen Saudiyya, Libya, Masar, Pakistan, Indiya da Moroko sukan shafe sa'o'i 15 basu sha ruwa ba.

Kasar Najeriya da kasar Senegal sukan shafe sa'o'i 14 suna azumi.

Kasar Kenya da Indonesiya kan shafe sa'o'i 13 basu yi buda baki ba.

Sai kuma kasar Australiya wacce ke shafe sa'o'i 11, yayin da kasar Chile kuma tafi ko ina karancin sa'o'in azumi, inda take da sa'a 10 kacal.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng