An bukaci masu azumi su ci abinci mai yawa lokacin sahur da buda baki saboda coronavirus

An bukaci masu azumi su ci abinci mai yawa lokacin sahur da buda baki saboda coronavirus

A yau Juma’a, 24 ga watan Afrilu, ne al’umman Musulmi a kasashen duniya ciki harda Najeriya, suka tashi da azumin watan Ramadana.

Sai dai kuma azumin bana ya riski bayin Allah a cikin wani yanayi na sai lahaula, sakamakon annobar da duniya ta tsinci kanta ciki.

Kamar yadda kuka sani, azumi na daya daga cikin ginshikan addinin Musulunci, kuma wajibi ne ga duk wani musulmi baligi mai cikakken lafiya, ya kame baki daga fitowar alfijir har zuwa faduwar rana.

An bukaci masu azumi su ci abinci mai yawan lokacin sahur da buda baki saboda coronavirus

An bukaci masu azumi su ci abinci mai yawan lokacin sahur da buda baki saboda coronavirus
Source: Facebook

Sai dai likitoci sun ce azumi mai tsayi na rage karfin garkuwar jiki, saboda haka sun shawarci mutane su ci abinci da kyau da shan ruwa mai yawa a lokutan buda baki da sahur.

An kuma bukaci mutane da su yawaita cin abubuwa masu gina jiki da kara karfin garkuwan jiki a lokacin bude baki da sahur.

Har ila yau masu azumi su lazumci shan sinadaren vitamin c da iron da kuma shan kayan marmari da ganyayyaki daban-daban.

KU KARANTA KUMA: Abba Kyari: An nemi Buhari ya kacaccala mukamin shugaban ma’aikatan shugaban kasa

Sannan marasa lafiya, ko wadanda suka harbu da annobar corona kar su dauki azumin.

Kasashen Musulmi da dama sun rufe masallatai, yayin da wasu suka dan sassauta dokar hana fita saboda watan Ramadana.

A wani labari na daban, mun ji cewa Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto ya kafa kwamiti mai mambobi 32 wadda za su raba wa alumma abinci lokacin azumin watan Ramadan ta hanyar bin dokokin kiyaye yaduwar COVID-19.

Sanarwar ta Tambuwal ya fitar ta bakin Kakakinsa, Muhammad Bello ya ce wannan tsarin ciyarwar yana da banbanci da irin wanda aka yi a shekarun baya kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Gwamnan ya ce masu rabon abincin za su bi dokokin da Cibiyar Lafiya ta Duniya, WHO, ta gindaya domin kare yaduwar cutar COVID-19 a tsakanin alumma.

Gwamnan ya kara da cewa adadin kudin da aka ware domin ciyarwar ya karu daga Naira miliyan 380 a bara zuwa N500 a bana saboda adadin masu bukata ya karu kuma farashin kayan abinci ya sauya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel