Najeriya Ta Koma Ba Nijar Wutar Lantarki Bayan Kungiyar ECOWAS Ta Ɗage Takunkumi

Najeriya Ta Koma Ba Nijar Wutar Lantarki Bayan Kungiyar ECOWAS Ta Ɗage Takunkumi

  • Bayan ɗage dukkanin takunkumi da kungiyar ECOWAS ta ƙaƙabawa kasashen Nijar, Mali da Burkina Faso, an ci gaba da kai wuta Nijar
  • A watan Agustan 2023 ne gwamnatin Najeriya ta katse kai wuta Nijar tare da rufe iyakokin ƙasa sakoda takunkumin ECOWAS
  • Sai dai wasu mazauna jamhuriyar Nijar da Legit Hausa ta zanta da su, sun bayyana cewa katse wutar tun farko bai yi wa kasar wata illa ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Najeriya ta amince ta maido da wutar lantarki a Jamhuriyar Nijar yayin da kungiyar ECOWAS ta dage takunkumin da ta kakaba wa Nijar, Mali da Burkina Faso da kuma Guinea.

An dage takunkumin ne bayan wani babban taron kungiyar ECOWAS kan harkokin siyasa, zaman lafiya da tsaro da aka gudanar a Abuja, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Rigima ta ƙara zafi a APC yayin da dakarun ƴan sanda suka ƙwace iko da sakateriya a jihar Arewa

Najeriya za ta ci gaba da kai wuta Nijar
Mazauna Nijar sun ce katse wutar bai wa kasarsu wata illa ba, domin wuta ba ta dauke ba. Hoto: @ecowas_cedeao
Asali: Twitter

Tsohon shugaban kasar Najeriya kuma wanda ya assasa kungiyar ECOWAS, Janar Yakubu Gowon (mai ritaya), ya shiga tsakani tare da sasanta rikicin ECOWAS da kashen uku.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Najeriya ta daina kai wuta Nijar a watan Agusta 2023

Ya kuma bukaci kasashen uku da su janye sanarwarsu na ficewa daga kungiyar ECOWAS, rahoton Premium Times.

A watan Agustan bara ne Najeriya ta katse wutar lantarki ga Jamhuriyar Nijar a matsayin daya daga cikin takunkumin da kungiyar ECOWAS ta kakaba wa kasar.

Sanatoci Arewa, a watan Nuwamban da ya gabata, sun bukaci shugaba Bola Tinubu da ya maido da wutar lantarki a Jamhuriyar Nijar.

Tinubu ya ba da umarnin dage takuntumi

A ranar 24 ga watan Fabrairu ne shugaban Najeriya Bola Tinubu, ya yi kira da a dage dukkan takunkumin tattalin arziki da aka kakabawa kasashen uku.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta dura kan 'yan Crypto, ta kakaba wa Binance tarar dala biliyan 10

Tinubu ya bukaci kungiyar ECOWAS da ta dawo da shigar da kayan abinci da magunguna da sauran kayayyakin jin kai ba tare da katsewa ba ga al’ummar wadannan kasashe.

Legit ta ji ra'ayin mazauna jamhuriyar Nijar kan lamarin

Idan muka ɗauki babban birnin ƙasar, Niamey, abubuwa sun yi yawa, buƙatun wuta sun fi ko'ina yawa, saboda haka sun samu matsalar ƙarancin wuta kamar yadda mazauna can suka shaida mana.

Sauran jihhohi suna da sauƙin lamura saboda abubuwa ukku; buƙatuwarsu ba ta kai ta Yamai ba, akwai injinoni waɗanda ake amfani da su idan an samu matsala, babu tsananin zafi.

Mani Kasumawa Kalgeri ya ce dab da juyin mulki, shugaban kasar Nijar, Bazoum ya sayo manyan injinan lantarki aka kafa a Damagaram, sannan ya sa katse wutar bai shafe su ba.

Awa 24 ba a dauke wuta a Nijar

Duk da hakan, Kalgeri ya ce yanzu da Najeriya ta dawo ba Nijar wuta, garuruwan da ba su da injina irin na Damagaram za su dawo samun wuta saɓanin lokacin da aka katse ta.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun dakatar da zanga-zangar NLC a Borno a kan wani dalili 1 tak

Ya ce:

"A tsarin ƙasa da ƙasa, Najeriya ce kawai ƙasar da ke ba Nijar wutar lantarki, amma gwanatin Bazoum da ta mulkin soja sun yi hobbasa wajen samar mana da tamu wutar a sassan ƙasar.
"Mu a Nijar yanzu mun saba ba a ɗauke wuta, kuma da taimakon Najeriya hakan take kasancewa, don haka mun ji dadin janye wannan takunkumin."

Yankunan da suka samu matsala

Abubakar Saddiq, mazaunin Zindar, Damagaram ya ce katse wutar da Najeriya ta yi tun farko bai yi wa Nijar illa ba, musamman a yankunan Zindar, Maradi, da sauran su.

"Yankunan da kawai abin ya fi shafa su ne Niamey, Tawa da Doso, su ma ba wai ya yi tsanani ba ne kuma wasu sassa ne na yankunan.

- Abubakar Saddiq, mazaunin Nijar

Yawan kasashen ECOWAS ya koma 15 bayan ɗage takunkumi

Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa yanzu yawan ƙasashen da ke cikin kungiyar ECOWAS ya koma 15 bayan dage takunkumin da aka ƙaƙabawa Nijar, Mali da Burkina Faso.

Kasashen uku sun fitar da sanarwar ficewa daga ECOWAS bayan da aka saka masu dokoki masu zafi, amma daga bisani kungiyar ta sassauta dokokin har ma ta janye su gaba daya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.