Sanatocin Arewa Sun Yi Martani Mai Daukar Hankali Bayan ECOWAS Ta Cire Takunkumi Kan Nijar

Sanatocin Arewa Sun Yi Martani Mai Daukar Hankali Bayan ECOWAS Ta Cire Takunkumi Kan Nijar

  • Wasu sanatoci a Najeriya sun ji dadin yadda ECOWAS ta dage takunkumin da ta daura kan jamhuriyar Nijar
  • An yi juyin mulki a Nijar a 2023, har yanzu ba a mayarwa ‘yan dimokradiyya mulki ba, lamarin da ke daukar hankali
  • Rahotanni sun bayyana maslahar da ECOWAS ta duba don dage wannan takunkumi da aka sanya a 2023

Salisu Ibrahim ne babban editan (Copy Editor) sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

FCT, Abuja - Sanatocin Arewacin Najeriya sun yabawa shugabannin ECOWAS bisa dage takunkumin da suka daurawa jamhuriyar Nijar a 2023.

Idan baku manta ba, an kakabawa shugabannin sojin Nijar takunkumin ne bayan yin juyin mulki a kasar da ke Arewa masu Yamma a ranar 26 ga watan Yulin 2023.

Kara karanta wannan

ECOWAS Ta Ɗage Takunkumi 8 Da Ta Ƙaƙabawa Jamhuriyar Nijar, Ta Bada Dalili

A wani taron da suka gabatar, shugabannin na ECOWAS sun bayyana dage takunkumin da suka kakabawa Nijar da ya hada da rufe iyakokin kasa, garkame asusun gwamnatin kasar da yanke alakar kasuwanci a kasashen ECOWAS.

Sanatocin Arewa sun ji dadin cirewa Nijar takunkumi
An cirewa Nijar takunkumi, sanatocin Arewa sun yabawa ECOWAS | Hoto: @officialABAT, @NigeriaSenate
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar rahoto, an cire takunkumin ne duba da halin da ‘yan kasar ke ciki, inda ake sa ran hakan zai farfado da al’amaru masu yawa.

Sanatocin Arewa sun magantu kan dage takunkumin

A bangare guda, Zauren Sanatocin Arewa ya bayyana yabo ga ECOWAS bisa wannan aiki na dage takunkumi, inda ya bayayana goyon baya ga hakan, Daily Trust ta ruwaito.

A cewar sanatocin, tabbas ECOWAS ta duba yanayi tare da martaba ‘yancin ‘danadam a wanan yunkuri.

Sun kuma bayyana cewa, tabbas dage wannan takunkumi zai rage radadin da ‘yan Nijar ke ciki na bayan juyin mulki, musamman ta fuskar tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Gowon ya sasanta rikicin ECOWAS da Nijar, Mali da Burkina Faso, za a janye masu takunkumi

A mayar da mulki hannun ‘yan dimokradiyya, inji sanatoci

Hakazalika, sun yi kira ga shugabannin sojin Nijar da su duba tare da mayar da mulki kan turbar dimokradiyya kamar yadda ake yi a baya, jaridar Vanguard ta tattaro.

Sun kuma bukaci masu ruwa da tsaki da ke tsakani da su kasance cikin tattaunawa kan yadda za a dinke duk wata baraka da ake fuskanta.

Tun bayan juyin mulkin Nijar aka samu cece-kuce da dama a bangarori daban-daban na nahiyar Afrika, musamman Najeriya mai makwabtaka da Nijar din.

ECOWAS ta dage takunkumi kan Nijar

A wani rahotonmu na baya, kunji yadda ECOWAS ta bayyana dage takunkumin da ta kakabawa jamhuriyar Nijar.

Wannan na zuwa ne bayan watanni da yin juyin mlkin da ya jawo sanya takunkumin tun farko a watan Yulin bara.

Kasashen Afrika na yawan fuskantar juyin mulkin soja, wanda ake ganin ya fi faruwa a kasashen renon Faransa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel