Yawan Ƙasashen da Ke Cikin ECOWAS Ya Koma 15 Bayan Dawowar Nijar, Mali da Burkina Faso

Yawan Ƙasashen da Ke Cikin ECOWAS Ya Koma 15 Bayan Dawowar Nijar, Mali da Burkina Faso

 • Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika (ECOWAS) ta dage takunkumin da ta kakabawa Nijar, Mali da Burkina Faso
 • Har ila yau, kungiyar ta janye dokar rufe duk wata hada-hadar kudi tsakanin kasashen ECOWAS da Nijar da bude iyakokin kasar
 • Binciken da Legit Hausa ta yi a shafin yanar gizon ECOWAS ya nuna cewa har yanzu kasashen uku na cikin jerin sunayen mambobin kungiyar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika (ECOWAS) ta dage takunkumin karya tattalin arzikin da ta kakabawa Nijar, Mali da Burkina Faso.

Hakan ya biyo bayan tattaunawar da hukumar ta ECOWAS ta dauki tsawon sa’o’i tana yi a wani taro na musamman da ta yi a fadar gwamnati da ke Abuja ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Rayuka 7 sun salwanta saboda turmutsitsi a wajen siyan shinkafar kwastam a jihar APC

Cikakken jerin kasashe 15 na ECOWAS.
Cikakken jerin kasashe 15 na ECOWAS. Hoto: @ecowas_cedeao
Asali: Twitter

Janye takunkumi a kan Burkina Faso, Mali da Nijar

Da yake sanar da matsayar kungiyar, shugaban hukumar ECOWAS, Dr Omar Touray, ya ce an dage dokar rufe iyakokin kasa da ta sama zuwa Nijar, The Nation ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har ila yau, kungiyar ta janye dokar rufe duk wata hada-hadar kudi tsakanin kasashen ECOWAS da Nijar tare da sakar wa kasar akalar asusun bankinta.

Channels TV ta ruwaito cewa, Burkina Faso, Mali da Jamhuriyar Nijar a ranar Lahadi, 28 ga watan Janairu, suka sanar da ficewa daga kungiyar ECOWAS.

Muhimmancin Burkina Faso, Mali da Nijar a ECOWAS

Kasashen uku, sun yi zargin cewa ECOWAS ta kaucewa akidar kakanninsu da kuma tsare-tsare na kishin Afirka.

Sai dai hukumar ta ECOWAS ta mayar da martani cikin gaggawa cewar ba ta da masaniyar ficewar kasashen ukun.

Kara karanta wannan

Sanatocin Arewa sun yi martani mai daukar hankali bayan ECOWAS ta cire takunkumi kan Nijar

ECOWAS ta kara da cewa Burkina Faso, Nijar, da Mali na da matukar muhimmanci ga kungiyar da kuma al'ummomin da ke cikin kungiyar.

Binciken da Legit Hausa ta yi a shafin yanar gizon ECOWAS ya nuna cewa har yanzu kasashen uku na cikin jerin sunayen mambobin kungiyar.

Ga cikakken jerin kasashen ECOWAS:

 1. Benin
 2. Burkina Faso
 3. Cabo Verde
 4. Cote D'Ivoire
 5. Gambiya
 6. Gana
 7. Guinea
 8. Guinea Bissau
 9. Laberiya
 10. Mali
 11. Nijar
 12. Najeriya
 13. Senegal
 14. Sierra Leone
 15. Togo

Ficewar Nijar, Mali da Burkina Faso zai jawo matsala a Afrika

Tun da fari, Legit Hausa ta tattaro bayani kan yadda ficewar Nijar, Mali da Burkina zai kawo babban cikas ga tattalin arziki da ci gaban kasashen Afirka ta Yamma.

Matsalolin da ƙasashen ECOWAS za su fuskanta sun hada da raguwar cinikayya saboda rufe iyakoki, matsalar tsaro saboda rashin taimakekeniyar dakarun soji.

Asali: Legit.ng

Online view pixel