An Saki Kayatattun Hotunan Masallaci Mafi Girma a Afrika Wanda Aka Bude a Aljeriya
- Kasar Aljeriya ta ƙaddamar da wani katafaren masallaci mafi girma a Afrika wanda ke iya daukar masallata 120,000 a lokaci guda
- Rahotanni sun bayyana cewa an fara ginin masallacin a shekarun 2010 amma saboda matsaloli na siyasa ya sa ba a kammala shi ba
- An kashe dala miliyan 898 wajen gina masallacin kuma yana da husumiya mafi tsayi a duniya mai ƙafa 859 (mita 265)
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Aljeriya ta kaddamar da wani katafaren masallaci a gabar tekun 'Bahar Rum' bayan shafe shekaru da dama ana fama da rikicin siyasa wanda ya kawo tsaiko wajen kammala shi.
Kamfanin dillancin labaran Associated Press ya bayar da rahoton cewa, shugaban kasar Aljeriya, Abdelmadjid Tebboune ne ya bude masallacin a ranar Lahadi.
Masallacin ne na uku mafi girma a duniya
A cewar The Guardian, wani kamfanin gine-gine na kasar Sin ne ya gina ‘babban masallacin Algiers’ a cikin shekarun 2010.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An ce masallacin yana dauke da husumiya mafi tsayi a duniya, mai tsayin mita 265 (kafa 869).
An ba da rahoton cewa shi ne masallaci na uku mafi girma a duniya, mafi girma a Afirka, kuma mafi girma a wajen manyan biranen Islama.
An kashe kudi har dala miliyan 898 wajen gina masallacin
Har ila yau, yana da bangaren saukar jirgi mai saukar ungulu da ɗakin karatu da zai iya ɗaukar littattafai har miliyan ɗaya.
Baya ga tsananin girmansa, masallacin ya yi kaurin suna saboda tarin jinkiri da cece-kuce da aka yi a lokacin gininsa na tsawon shekaru bakwai.
A hukumance, an kashe tsabar kudi har dala miliyan 898 wajen gina masallacin wanda ya ke iya daukar mutane dubu 120 a lokaci guda.
Kalli hotunan a kasa:
Tsohon shugaban kasar Abdelaziz Bouteflika ne ya kaddamar da aikin masallacin da nufin ganin ya zama mafi girma a Afirka.
Ya yi burin ya zama wata gudunmawa da ya bayar ga addini, kuma ya so ya sanya masa suna "Masallacin Abdelaziz Bouteflika," kamar Masallacin Hassan II a Casablanca, Maroko.
Hotunan kayatattun masallatai 5 mafi kyau a duniya
A hannu daya, Legit Hausa ta kawo maku bayani game da wasu manyan masallatai mafi kyawun gani a duniya, kamar yadda binciken masana ya nuna.
Na farkon su shi ne Masallacin Harami yayin da na ƙarshen su shi ne masallacin Sultan Brunei da ke birnin kasar Brunei, kuma dukkan masallatan biyar na samu ziyartar mutane.
Asali: Legit.ng