Dubi jerin birane 10 mafi wahalar zama a duniya a shekarar 2021

Dubi jerin birane 10 mafi wahalar zama a duniya a shekarar 2021

An sanya Legas, cibiyar kasuwancin Najeriya a matsayin birni na biyu mafi wahalar zama a duniya, bisa ga alkaluman birane mafi sauki da mafi gajiyarwa na 2021 wanda VAAY.com ta fitar.

Kididdigar ta tsara biranen 100 ta hanyar lura da abubuwa kamar aminci da tsaro, kwanciyar hankali na siyasa da zamantakewa, yawan jama'a, iska, hasken wuta, da matakan hayaniya, yawan cunkoson ababen hawa da yanayin gari don ƙayyade matakan gajiyarwar.

KU KARANTA KUMA: Sace dalibai: Mun samu labarin shige da ficen ‘yan bindiga amma sun sha kan jami’an tsaro – Gwamna Bagudu

Dubi jerin birane 10 mafi wahalar zama a duniya a shekarar 2021
Legas ce ta biyu a jerin birne mafi wahalar zama a duniya a shekarar 2021 Hoto: PIUS UTOMI EKPEI/AFP
Asali: Getty Images

Sauran abubuwan da aka yi la’akari da su sun hada da yawan rashin aikin yi, shugabanci, da kuma lafiyar kwakwalwa.

Har ila yau, a Afirka, Alkahira ta Masar ta zama ta 13, garin Dakar na Senegal ya kasance na 17 yayin da Nairobi na Kenya ya zauna a matsayi na 21.

Garin da ya zamo na daya wajen wahalar zama shine Mumbai a Indiya.

Birane goma da suka fi wahalar zama a 2021

1. Mumbai, Indiya

2. Legas, Najeriya

3. Manila, Philippines

4. New Delhi, Indiya

5. Baghdad, Iraq

6. Kabul, Afghanistan

7. Moscow, Rasha

8. Karachi, Pakistan

9. Jakarta, Indonesia

10. Kiev, Ukraine

A gefe guda, Reykjavik, wani birni a Iceland, ya zama birni mafi ƙarancin damuwa a duniya a cikin 2021.

Garuruwan goma mafi ƙarancin damuwa a cikin 2021

1. Reykjavik, Iceland

2. Bern, Switzerland

3. Helsinki, Finland

4. Wellington, New Zealand

5. Melbourne, Ostiraliya

6. Oslo, Norway

7. Copenhagen, Denmark

8. Innsbruck, Austria

9. Hanover, Jamus

10. Graz, Austria

Jihar Kano da Legas na da matukar muhimmanci ga Najeriya, Inji Asiwaju Bola Tinubu

A wani labari na daban, jagoran jam'iyyar APC na ƙasa, Bola Tinubu yace ya zama wajibi jihar Kano da jihar Lagos su cigaba da kasancewa cikin zaman lafiya saboda yawan al'ummar su da tattalin arziƙinsu.

Tinubu ya bayyana haka ne ranar lahadi lokacin da yakai ziyara fadar mai martaba sarkin Kano, Aminu Ado Bayero, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Wannan ziyara tasa na daga cikin ayyukan da yake yi na bikin zagayowar ranar haihuwarsa, ya cika shekaru 69 a duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng