“Kudin Hayar Wata 1 a UK Shine Na Shekara 1 a Najeriya”: Wani Mutum Da Ke Zaune a Birtaniya Ya Buga Lissafi

“Kudin Hayar Wata 1 a UK Shine Na Shekara 1 a Najeriya”: Wani Mutum Da Ke Zaune a Birtaniya Ya Buga Lissafi

  • Wani dan Najeriya da ke zama a kasar Birtaniyya ya ayyana cewa zaman UK ba na masu raunin zuciya bane
  • A wani bidiyo da ya yadu, mutumin ya ce kudin hayar wata daya a UK na iya karbarwa mutum hayar shekara daya a Najeriya
  • Bidiyon ya haifar da martani tsakanin masu amfani da TikTok, da dama sun yarda da hasashensa, amma wasu basu yarda ba

Wani dan Najeriya da ke zaune a UK ya ce kudin hayar shekara daya a Najeriya zai iya biyan hayar wata daya ne kawai a UK.

A wani bidiyo da Demopumpin ya wallafa, an gano mutumin yana wasu lissafe-lissafe kan tsadar gida a UK.

Matashi ya bayyana tsadar kudin haya a UK
“Kudin Hayar Wata 1 a UK Shine Na Shekara 1 a Najeriya”: Wani Mutum Da Ke Zaune a Birtaniya Ya Buga Lissafi Hoto: TikTok/@demopumpin.
Asali: TikTok

Demopumpin ya ayyana cewa zaman UK ba na masu rauni bane saboda tsadar kudin gida.

Dan Najeriya ya koka kan tsadar gida a UK

Kara karanta wannan

Allah Daya Gari Banban: Dan Najeriya Ya Saka Siket Zuwa Wajen Daurin Aurensa, Bidiyon Ya Yadu

Ya yi mamakin dalilin da yasa kudin haya ke da tsada sosai a UK idan aka kwatanta da Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutumin ya yi tunanin ko dai zai fi masa idan ya dawo Najeriya ko ya ci gaba da zama a UK.

Wani binciken yanar gizo da Legit.ng ta yi ya nuna cewa hida mai daki daya a Landan yana kai wa fan 2000 duk wata, wanda ya fi naira miliyan 1.9.

Yayin da mutane da dama suka yarda cewa hayar gida na da tsada a UK, wasu sun ce albashin chan na da yawa shima.

Kalli bidiyon a kasa:

Martanin jama'a yayin da wani mutum ke kwatanta tsadar kudin gida a Najeriya da UK

Wonderboy ya tambaya:

"Ta yaya albashinka na wata daya a UK ya zama kudin da wani zai shafe shekaru biyu yana tarawa a Najeriya?"

Kara karanta wannan

“Budurwarsa Ta Ba Shi Kunya”: Malamin Addini Ya Yi Tsalle Daga Ginin Bene Mai Hawa 2, Ya Mutu a Anambra

@user622126580390 Ya ce:

"Shekara daya a Lekki. Saboda kudin da nake biya kan daki daya duk wata a Gabashin Landan zai iya isar mutum jari a Najeriya."

@Correct Dude ya ce:

"Kudin hayar gida mai dakuna uku a Najeriya na shekara daya shine kudin hayar daki daya a UK."

Budurwa ta shiryu, ta kona kayanta masu nuna tsaraici

A wani labarin, mun ji cewa wata matashiyar budurwa ta saki bidiyo da ke nuna lokacin da ta kona gaba daya kaya masu nuna tsaraici da ta mallaka.

A bidiyon da aka wallafa a ranar Asabar, 27 ga watan Agusta, Precious Thamani ta ce ta yanke shawarar zama kirista ta gaske.

Asali: Legit.ng

Online view pixel