Filin Jirgin Saman Minna Na Gab Da Fara Aiki, Gwamna Bago

Filin Jirgin Saman Minna Na Gab Da Fara Aiki, Gwamna Bago

  • Gwamnatin jihar Neja ta fara tattaunawa da kamfanonin jiragen sama domin farfado da zirga-zirga a filin jirgin sama na garin Minna
  • Gwamna Mohammen Umaru Bago ne ya bayyana haka yayin da ya kai ziyarar gani da ido da tuba yadda aikin gyaran titin jirgin ke gudana
  • Bago ya ce gwamnatinsa na duba yiwuwar karbar aikin daga hannun da kwangilar da ke yinsa duba ga yadda lamarin ke tafiyar hawainiya

Nihar Neja - Gwamna Mohammed Umaru Bago na jihar Neja ya bayyana cewa gwamnati ta fara tattaunawa da kamfanonin jirage masu zaman kansu domin fara jigilar jirage a filin jirgin sama na Abubakar Imam da ke garin Minna.

Ya yi jawabi ne yayin da yake duba aikin sake gina titin jirgin da tasha a filin jirgin, jaridar Leadership ta rahoto.

Kara karanta wannan

Gwamnati Ta Dakatar Da Wani Babban Basarake Saboda Rashin Biyayya A Wata Jiha, Bayanai Sun Fito

Gwamnatin Bago na shirin farfado da filin jirgin sama na Minna
Filin Jirgin Saman Minna Na Gab Da Fara Aiki, Gwamna Bago Hoto: Umaru Mohammed Bago
Asali: Facebook

Jirage na gab da fara zirga-zirga a filin jirgin saman Minna

Bago wanda ya nuna damuwarsa kan yadda ake tafiyar hawainiya da aikin tashar, ya ce gwamnatin jihar za ta gayyaci dan kwangilar tare da duba yadda za ta karbi aikin domin kammala shi cikin gaggawa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce kammala aikin tashar zai sa jiragen yan kasuwa fara gudanar da ayyukan zirga-zirga.

Ya ce:

“A matsayinmu na gwamnatin jiha muna so mu gayyaci dan kwangilar domin ganin yadda za mu shiga cikin lamarin sannan kuma idan zai yiwu mu karbi aikin domin mu samu filin jirgin sama mai aiki.
"Burinmu ne samar da jiragen kasuwanci kuma muna tattaunawa da wasu kamfanonin jiragen sama masu zaman kansu da su zo jihar."

A kan aikin titin jirgin, gwamnan ya nuna jin dadinsa da irin ingancin ayyukan da aka yi, ya kuma ce yana da yakinin cewa za a mika aikin kafin ranar 15 ga watan Agusta, rahoton Nigerian Tribune.

Kara karanta wannan

Sojojin Nijar Sun Aikawar Da Wata Sabuwar Doka A Kasar, Janar Tchiani Ya Yi Bayani

Dan kwangilar da ke kula da aikin titin jirgin ya ba da tabbacin cewa zai cimma ranar domin za a shimfida kwalta a ranar Talatar mako mai zuwa kuma zai kammalu domin jirgi ya sauka a kansa daga ranar 16 ga watan Agusta.

Gwamna Bago ya bai wa dan Igbo mukami a gwamnatinsa

A wani labari na daban, mun ji cewa yan kwanaki bayan yan kabilar Ibo mazauna jihar Neja sun bukaci a basu gurbi a majalisar Gwamna Mohammed Bago, gwamnan ya nada Mista George Dike a matsayin mai ba shi shawara na musamman kan harkokin kabilu.

Gwamnan ya kuma nada wasu mutum 25 a matsayin masu ba shi shawara na musamman a bangarori daban-daban. Sunayen ya kunshi mata da maza daga jihar.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel