Rwanda, Kamaru Sun Yi Wa Jami'an Tsaronsu Garambawul Bayan Juyin Mulkin Gabon

Rwanda, Kamaru Sun Yi Wa Jami'an Tsaronsu Garambawul Bayan Juyin Mulkin Gabon

  • Tun bayan juyin mulki a kasar Gabon, kasashen Nahiyar Afirka da dama su ka shiga taitayinsu
  • Wannan na zuwa ne bayan juyin mulki a Jamhuriyar Nijar da kuma kasar Gabon a jiya Laraba 30 ga watan Agusta
  • Kasashen Rwanda da Kamaru sun dauki matakan yin garambawul a rundunonin tsaron kasashensu

Biyo bayan juyin mulki a kasar Gabon kasashen Afirka da dama sun shiga taitayinsu ganin cewa abin na iya faruwa a kasashensu.

Dalilin haka, kasashen Rwanda da Kamaru sun yi sauye-sauye a rundunar tsaronsu tare da yi wa manyan sojoji ritaya.

Kamaru da Rwanda sun yi garambawul ga rundunar sojoji a kasashensu
Rwanda, Kamaru Sun Yi Sauye-Sauye A Rundunar Tsaronsu Yayin Da Juyin Mulki Ke Yaduwa A Afirka. Kagame/Paul Biya.
Asali: Getty Images

Wani mataki Rwanda ta dauka bayan juyin mulki?

Shugaba Paul Kagame na Rwanda ya yi wa manyan sojoji ritayar dole tare da bai wa matasa dama, TRT Africa ta tattaro.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Juyin Mulkin Gabon: Atiku Ya Bayyana Yadda Za Kawo Karshen Kwace Mulki Da Sojoji Ke Yi a Afrika

Sannan Kagame ya ba da umarnin nada janar-janar da za su jagoranci rundunar tsaron kasar a bangarori da dama.

A cikin wata sanarwa da aka fitar a jiya Laraba 30 ga watan Agusta na cewa:

"Kagame ya amince a yi ritaya ga janar-janar, da manyan sojoji 83 da kuma kananan sojoji shida.”

Har ila yau, Kagame ya bayar da umarnin yi wa sojoji 86 ritaya kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Wani mataki Kamaru ta dauka bayan juyin mulki?

Tun da farko a ranar ta Laraba, Kagame ya yi karin girma ga wasu matasan sojoji zuwa mukaman Kanar sannan ya nada wasu janar-janar don shugabantar wasu rundunonin soji, cewar Business Day.

A watan Yuni, Kagame ya nada Juvenal Marizamunda a matsayin ministan tsaro, inda ya maye gurbin Albert Murasira, wanda ke kan mukamin tun 2018.

A daya bangaren kuma, shugaban Kamaru Paul Biya, daya daga cikin wadanda suka fi dadewa a kan mulki a Afirka, ya yi sabbin nade-nade a Ma'aikatar Tsaron kasar.

Kara karanta wannan

Ku kama kanku: Kungiyar AU ta fusata da juyin mulkin Gabon, ta gargadi sojoji

Wata majiya daga rundunar sojin kasar ta tabbatar da haka a shafukan intanet inda ta ce garambawul din bai rasa nasaba da yaduwar juyin mulki a Nahiyar Afirka.

Sojoji Sun Kifar Da Gwamnatin Gabon

A wani labarin, a safiyar jiya Laraba 30 ga watan Agusta, an wayi gari da labarin juyin mulki a kasar Gabon.

Sojin kasar sun kifar da gwamnatin Ali Bongo wanda ya shafe shekaru 12 ya na mulkin kasar tun bayan rasuwar mahaifinsa Omar Bongo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel