Wasu Jiragen Yakin Kasar Amurka Sun Yi Hadari a Sararin Samaniya

Wasu Jiragen Yakin Kasar Amurka Sun Yi Hadari a Sararin Samaniya

  • Wasu jiragen yaƙin sojin Amurka sun gamu da haɗari a sararin samaniya, a yayin atisayen koyon tuƙi
  • Jiragen yaƙin sun yi taho mu gama ne a yankin Healy na birnin Alaska a Amurka ranar Alhamis
  • Sojoji uku sun sheƙa barzahu, yayin da wani ɗaya kuma ya samu raunika a haɗarin na kwana-kwanan nan

Kasar Amurka - Wasu jiragen yaƙin sojin Amurka guda biyu sun yi taho mu gama a yayin wani atisayen koyon tuƙi, a ranar Alhamis a birnin Alaska na ƙasar.

Rundunar soji ta tabbatar da aukuwar haɗarin wanda ya ke kasance irin sa na biyu a cikin ƙasa da wata ɗaya a ƙasar, cewar rahoton Punch

Jiragen yakin Amurka guda 2 sun yi hadari
Jiragen yakin AH-64 (ba da su aka yi hadarin ba) Hoto: Alakapublicmedia.com
Asali: UGC

A wata sanarwa da bataliya ta 11 ta Airborne division ta fitar, ta bayyana cewa jiragen suna kan hanyar su ta dawowa daga atisayen koyon tuƙi ne lokacin da lamarin ya auku.

Kara karanta wannan

Bayin Allah Da Dama Sun Jikkata, Dukiyoyi Sun Salwanta a Wani Mummunan Fada Da Ya Barke a Jihar Arewa

Sanarwar na cewa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Jirage masu saukar ungulu na AH-64 Apache sun yi haɗari yau a kusa da Healy, a Alaska yayin da su ke dawowa daga atisayen koyon tuƙi. Masu bayar da agajin gaggawa suna wajen. Ana cigaba da bincike kan lamarin sannan za a saki ƙarin bayani idan an samu."

Fox news tace sojoji uku suka rasu a haɗarin, yayin da soja ɗaya ya samu rauni. Kowane daga cikin jiragen yana ɗauke da mutum biyu ne a cikin sa.

Lamarin ya biyo bayan wani haɗari da ya auku a ƙarshen watan Maris inda wasu jiragen yaƙi masu saukar ungulu, Blackhawk na rundunar sojin Amurka, suka haɗe a Kentucky, inda nan ta ke mutum 9 da ke cikin jiragen suka ce ga garin ku nan.

Ana yawan samun haɗarin jiragen yaƙi a Amurka

Kara karanta wannan

Gaskiya Ta Bayyana Kan Dalilin Da Ya Sanya Shugaba Buhari Ya kasa Cika Wasu Alkawuran Da Ya Yi Wa 'Yan Najeriya

A cikin ƴan shekarun nan an samu haɗarurrukan jiragen yaƙin ƙasar Amurka, ko a watan Fabrairu wani jirgin yaƙin Blackhawk yayi haɗari a yayin atisayen koyon tuƙi a Alabama, inda mutum biyu suka halaka.

Haka a shekarar da ta gabata, sojojin Amurka huɗu sun mutu a ƙasar Norway lokacin da jirgin su ƙirar V-22B Osprey ya kifo ƙasa, masu bincike sun ce ana tunanin ya tunkuyi tsauni ne.

Jirgin Sama Ɗauke da Fasinjoji Ya Yi Saukar Gaggawa a Abuja

A wani rahoton na daban kuma, kun ji cewa wani jirgin sama ya yi saukar gaggawa ba shiri a birnin tarayya Abuja.

Jirgin mai ɗauke da fasinjoji da dama, ya samu matsala ne a sararin samaniya wacce ta tilasta masa saukar gaggawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel