‘Yan Obidients Sun Shirya Zanga-Zangar Zaben 2023 a Fadar Shugaban kasar Amurka

‘Yan Obidients Sun Shirya Zanga-Zangar Zaben 2023 a Fadar Shugaban kasar Amurka

  • Mutanen Najeriya sun damar shirya zanga-zangar lumana a gaban gidan White House a Amurka
  • Za ayi zanga-zanga a fadar shugaban kasa domin nuna rashin jin dadin sakamakon zaben Najeriya
  • APC ta reshen Amurka ta ce ba kowa ba ne ya shirya wannan aiki illa ‘Dan takaran LP, Peter Obi

America - Wasu ‘yan Najeriya da ke kasar Amurka sun samu damar gudanar da zanga-zanga a fadar shugaban kasa da aka fi sani da White House.

A rahoton da muka samu daga The Cable, za ayi zanga-zangar ne a ranar 3 ga watan Afrilun 2023 domin a nuna rashin jin dadin nasarar yin Bola Tinubu.

Masu zanga-zangar su na bakin ciki da Bola Tinubu ya samu nasara a zaben shugaban kasa da aka yi, ya doke jam'iyyun PDP da LP a zaben bana.

A wani jawabi da ya fito daga bakin shugaban jam’iyyar APC na reshen Amurka, Tai Balofin ya fadawa mutanen Najeriya da su kwantar da hankalinsu.

Tai Balofin ya yi martani

Tai Balofin ya ce ka da jama’a su damu da zanga-zangan da ake shirin yi, ya kuma tabbatar da cewa gwamnatin Amurka ba ta goyon bayan lamarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban jam’iyyar yake cewa a kasar Amurka, kowa yana da damar da zai shirya zanga-zangar lumuna, saboda haka wannan ba matsala ba ce ga APC.

‘Yan Obidients
Tattakin masoyan Peter Obi Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

Balofin ya zargi ‘dan takaran shugaban kasa a karkashin jam’iyyar LP a zaben 2023 watau Peter Obi da hannu a wannan zanga-zanga da za a shirya.

Jaridar ta nemi jin ta bakin Kakakin LP, Yunsusa Tanko domin jin ta bakinsa, ba a dace ba.

"Babu abin da zai faru' - APC

"Ya na da muhimmanci a sani cewa gwamnatin Amurka ba ta da hannu ko kuma goyon bayan zanga-zangar, domin kowa yana iya yin zanga-zangar lumuna.
Mun yi imani cewa an yi adalci da gaskiya a zaben shugaban kasar Najeriya kuma Asiwaju Bola Tinubu ya yi nasara, mafi yawan jama’a sun kada masa kuri’a.
Babu abin da zai hana rantsar da Tinubu, Mu na tabbatar da cewa Najeriya ba za ta rabe ba, za ta cigaba da zama a dunkule, dole mu yi aiki tare domin ceton kasa."

- Tai Balofin

Binciken Diezani Alison-Madueke

An samu labari cewa takardun koti daga ma'aikatar shari'ar ƙasar sun nuna cin hancin da aka ba Diezani Alison-Madueke domin ta bada kwangiloli.

A lokacin ta na Minista, Diezani Alison-Madueke ta bada kwangilolin miliyoyin daloli bayan ta karbi rashawar Kolawole Aluko da Olajide Omokore.

Asali: Legit.ng

Online view pixel