"Bamu Ba Kai": Mutumin Da Ya Tsere Ya Bar Matarsa Da Da Tsawon Shekaru 33 Ya Dawo, Ya Nemi Wani Kason Gidansu

"Bamu Ba Kai": Mutumin Da Ya Tsere Ya Bar Matarsa Da Da Tsawon Shekaru 33 Ya Dawo, Ya Nemi Wani Kason Gidansu

  • Liu Yusheng ya tashi daga China zuwa Amurka shekaru 30 da su ka wuce, ya bar matarsa da yarinya yar shekara takwas
  • Lokacin da ya ka sa samun aiki, ya dawo Shangai, da nufin dawowa wajen matarsa da yarsa bayan shekara 30
  • Ya tarar gidan da ya bar su ciki hukuma ta rushe kuma an biya su da wani
  • Liu ya bukaci matar da bari ya zauna a banagaren gidan da ke Shanghai ko ta biya shi rabin kudin hayar gidan ko ya dauki matakin shari'a in taki amincewa

Wani mutum da ya bar iyalinsa don neman kyakkyawar makoma ya dawo, ya na so a ba shi rabin kadararsu.

Dan kasar China Liu Yusheng ya bar matarsa da yarsa yayin da ya gudu kasar Amurka ba bisa ka'ida na shekaru 30 da suka wuce.

Kara karanta wannan

Magidancin Da Aka Zarga Da Auren Karamar Yarinya Ya Yi Karin Haske, Ya Ce An Gina Auren Ne Kan Soyayyar Juna

Liu Yusheng
Mutumin Da Ya Tsere Ya Bar Matarsa Da Da Tsawon Shekaru 33 Ya Dawo, Ya Nemi Wani Kason Gidansu. Photo: South China Morning Post
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An sace fasfo, da kudin dan China a Amurka

Mutumin mai shekaru 73 wanda ya gudu Amurka tare da dan uwansa, da nufin samun ingantacciyar rayuwa, bai saka jin halin da iyalinsa ke ciki ba, kamar yadda South China Morning Post ta ruwaito.

Ya yi ikirarin cewa an sace ma sa fasfo da kudinsa, bai kuma samu aiki ba tsahon shekarun, sannan a titi ya ke kwana.

Da Liu ya dawo Shangai a watan Nuwambar 2022, bai iya gano inda matarsa da yarsa su ke ba.

Kungiyar yan Shanghai a Amurka

Kungiyar yan Shanghai mazauna Amurka su taimaka ma sa ya dawo dawo gida tare da taimaka ma sa ya samo adireshin matarsa da yarsa, amma iyalan na sa sun ki magana da shi.

Liu ya tuna cewa lokacin da ya tafi Amurka, hukumar kasar da ya ke aiki da ita ta ba shi gida wanda ya ke zaune da iyalansa.

Kara karanta wannan

Masu Garkuwa Sun Sace Yar Shekara 5 Da Matasa Biyu a Jihar Kwara

Hukumomi sun rushe gidansa na Shanghai

Sai dai, an rushe gidan bayan shekaru, kuma hukuma ta biya iyalan da gidan da ya fi wancan girma.

Liu ya bukaci matarsa da ta bari ya zauna a rabin gidan a Shanghai ko ta biya shi rabin kudin gidan.

Yanzu haka, da ya ke zaune a matsugunin gwamnati a Shanghai, Liu ya yi barazanar daukar matakin shari'a idan matarsa taki amincewa da bukatunsa.

Matarsa ba ta mayar da martani a bayyane kan barazanar mijinta, wanda ya gudu ya bar ta da yarinya mai shekaru takwas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel