Janar Buhari Ya Kori Baffana daga Aiki a Kan Canza Kudi a 1984 Inji Tsohon Amininsa

Janar Buhari Ya Kori Baffana daga Aiki a Kan Canza Kudi a 1984 Inji Tsohon Amininsa

  • Injiniya Buba Galadima ya ce kan batun canjin kudi Janar Muhammadu Buhari ya tsige kawun shi
  • Babban ‘dan siyasar ya ce Gwamnatin Buhari ta tsige baffansa Hassan Albadawi daga mukaminsa
  • Albadawi ya rasa aikinsa saboda ya roki a kara lokaci domin mutane su iya canza kudinsu a 1984

Abuja - Buba Galadima wanda yanzu jigo ne a jam’iyyar adawar nan ta New Nigeria People’s Party (NNPP) ya yi magana a kan tsarin canjin kudi.

Da aka zanta da Injiniya Buba Galadima a tashar talabijin Trust TV, ya bada labarin yadda kawunsa ya rasa aikinsa a mulkin Muhammadu Buhari.

Galadima ya ce baffansa da ya yi Kwamishinan ilmi a tsohuwar jihar Borno ya taba rokon Janar Muhammadu Buhari ya kara wa’adin canjin kudi.

An zanta ne da 'dan adawar a wani shirin siyasa, a nan ya dauko tarihin Hassan Albadawi.

Kara karanta wannan

Akwai Gwamna a Arewa da ya Boye Naira Biliyan 22 na Tsofaffin Kudi – Buba Galadima

Canza takardun kudi a 1984

Injiniya Galadima wanda ya yi aiki kut-da-kut da Buhari kafin ya zama shugaban kasa, ya ce shi ya raba kawunsa da aikinsa a lokacin mulkin soja.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kamar yadda aka yi a wannan karo, Gwamnatin Janar Buhari ta yi canjin kudi yayin da ya yi mulki tsakanin 1983 da 1985 wanda ya jefa wasu a matsi.

Buhari
Janar Buhari a jeji Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Ganin ya yi aiki da Buhari a lokacin yana Gwamna, Kantoman Gamboru Ngala a jihar Borno ya nemi alfarma domin karawa mutane wa’adin canza kudi.

A dalilin alfarmar da Albadawi yake nemawa mutanensa da ke nesa da banki, aka sauke shi daga mulki, Galadima ya ke fadawa gidan yada labaran

Tsige Hassan Albadawi nan take

“…Hassan Albadawi ya rike Kwamishina na ilmi a lokacin da shi (Janar Muhammau Buhari) yake Gwamna a jihar Arewa maso gabas,

Kara karanta wannan

Abin Da Ya Sa Na Ki Karbar N150m Da Motar N80m Don In Bar Atiku, Naziru Sarkin Waka

Daga baya ya zama Kantoman Gamboru Ngala da ke iyaka da Chad da Kamaru, ya fito talabijin ya roki a tsawaita wa’adin canjin kudi.
Yana so a kara wa’adin domin mutanensa ba su da banki. Kafin a gama labaran, sanarwa ta fito an tsige Kantoman wannan gari.

- Buba Galadima

Batun cewa akwai wadanda suka boye kudi gaskiya ne, a wani rahoto da aka fitar, an ji Buba Galadima ya yarda da gwamnatin Muhammadu Buhari.

'Dan siyasar yake cewa ya san akwai wani Gwamna a yankin Arewa maso yamma, wanda bayanan sirri sun tabbatar da yana da N22bn a gidansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel