Amurka Tayi Wa Matasan Najeriya Huduba, Ta Fada Masu Wanda Za Su Zaba a 2023

Amurka Tayi Wa Matasan Najeriya Huduba, Ta Fada Masu Wanda Za Su Zaba a 2023

  • Jami’ar kasar Amurka tayi magana a kan goyon baya wani ‘Dan Takara a zaben Shugaban kasa
  • Molly Phee ta ce Amurka da kasashen yamma ba marawa wani baya ya zama Shugaban Najeriya
  • Mataimakiyar Ministar harkokin Afrika ta Amurka ta fadawa matasa burinsu ayi zaben adalci

Lagos - Mataimakiyar Ministar harkokin Afrika ta kasar Amurka, Molly Phee ta tsoma baki a game da zaben shugabannin kasa da za ayi a Najeriya.

Vanguard ta rahoto Molly Phee tana cewa kasar Amurka ko sauran kasashen yammacin Turai da ake kawance da su, ba su da ‘dan takara a zaben.

Misis Molly Phee mai shekaru 60 ta ke cewa Amurka ko wata kasar ketare ba ta da iko a kan wanda za a zaba a ranar 25 daga watan Fubrairun 2023.

Kara karanta wannan

Matsaloli Sun Dabaibaye Kasa: Shugaba Buhari Zai Jagoranci Zaman Majalisar Magabatan Najeriya Yau Juma'a

Mataimakiyar Ministar ta ce abin da suke nema shi ne su ga an shirya zaben gaskiya na adalci, a samu sakamakon zaben da kowa zai yi alfahari da shi.

Jakadancin kasar Amurka tayi taro

Bayanin ya fito daga jami’ar ne a wajen wani taro da ofishin Jakadancin Amurka ta shirya mai taken shigo da matasa cikin harkar zabe a Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton ya nuna a ranar Alhamis Jakadancin ya shirya taron a garin Ikeja da ke jihar Legas.

Molly Phee
Molly Phee Hoto: diplomatictimes.net
Asali: UGC

Jami’ar kasar Amurkan tayi kira ga matasan Najeriya da su shirya kawo gyara a kasarsu ta hanyar mallakar katin PVC, sannan su tafi da murya daya.

Phee ta fadakar da matasan kasar nan cewa su zabi shugabannin da suka cancanta a zabe mai zuwa domin su ne wadanda za a bar wa rikon kasar nan gaba.

Kara karanta wannan

2023: APC na kitsa yadda za su sa kiristoci su tsane ni, Atiku ya tono sirrin 'yan APC

Jawabin Molly Phee ga matasa

“Ba mu goyon bayan wani mutum guda. Kasar Amurka ba ta da ‘dan takaran da take marawa baya a zaben shugaban kasar Najeriya.
Muna goyon bayan mulkin farar hula ne. Najeriya ta na da muhimmanci, shiyasa Amurka za ta taimaka ayi zaben aminci.
Ku ne manyan goben Najeriya. Matasa za su iya canza kasar nan. Ba ku bukatar Kasar Amurka kafin ku iya yi wa kan ku aiki.”

- Molly Phee

Guardian ta ce Ayo Makun (AY); Tauraron Big Brother Naija, Olamilekan Agbeleshe (Laycon); da Kafayat Shafau sun halarci wannan taro da aka yi.

Babu wanda ya cancanta irin Peter Obi

Barista Julius Nnamani ya fito yana cewa mutum daya ne daga Kudancin Najeriya wanda ya cancanta da mulki idan aka duba irin abubuwan da ya yi.

An rahoto ‘Dan siyasar yana cewa a ‘yan takaran shugaban kasa a zabe mai zuwa, Peter Obi na LP ne kawai zai iya maganin bashin da ke kan Najeriya.

Kara karanta wannan

Kasa Ta Yamutse, Shugaba Buhari Ya Kira Taron Gaggawa na Majalisar Koli a Najeriya

Asali: Legit.ng

Online view pixel