Shugaba Buhari Zai Jagoranci Zaman Majalisar Magabatan Najeriya Yau Juma'a

Shugaba Buhari Zai Jagoranci Zaman Majalisar Magabatan Najeriya Yau Juma'a

  • Da alamun lamarin Naira da tsadar mai sun tilasta shugaba Buhari son jin shawaran magabatansa
  • Majalisar magabata wata cibiya ce ta gwamnatin Najeriya wacce ke baiwa shugaban kasa shawara kan lamura masu muhimmanci
  • Wasu gwamnoni sun shigar da gwamnatin tarayya kara kotu kan lamarin wa'adin tsaffin Naira

Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari ya kira taron majalisar magabatar Najeriya domin tattaunawa kan abubuwan da suka shafi tsadar man fetur, karancin Naira, rashin tsaro da sauransu yayinda ake shirin zaben 2023.

Wannan taro zai gudana ne yau Juma'a, 8 ga watan Febrairu, 2023 misalin karfe 10 na safe.

Daily Trust ta ruwaito cewa gwamnan babban bankin Najeriya CBN na cikin wadanda aka gayyata wannan taro mai muhimmanci.

Ana sa ran zai zo ya yiwa majalisar bayani game da lamarin sauyin fasalin Naira.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Buhari na ganawar sirri da gwamnan CBN bayan hukuncin kotun koli kan batun kudi

Council
Shugaba Buhari Ya Kira Taron Gaggawa Na Dukkan Magabatan Najeriya Hoto: Presidency
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Majiyoyi daga fadar shugaban kasa sun bayyana cewa an gayyaci Shugaban hukumar zabe INEC da, Farfesa Mahmoud Yakubu, da Sifeto Janar na yan sanda, Usman Alkali Baba.

Zasu bayani ne game da irin shirin da suka yi wa zaben shugaban kasan ranar 25 ga Febrairu da kuma na gwamnoni ranar 11 ga Maris.

An tattaro cewa a zaman, za'a yanke shawara kan wasu abubuwa domin kwantar da hankulan jama'a gabanin zabe da kuma kawar rikici da ka iya aukuwa idan lamarin karancin Naira yayi kamari.

Majalisar magabata wata cibiya ce ta gwamnatin Najeriya wacce ke baiwa shugaban kasa shawara kan lamura masu muhimmanci.Majalisar magabata wata cibiya ce ta gwamnatin Najeriya wacce ke baiwa shugaban kasa shawara kan lamura masu muhimmanci.

Mambobin majalisar sun hada Shugaban kasa Muhammadu Buhari, mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, da sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Shugaban INEC Na Ganawa Da Buhari, Majalisar Zartaswa Kan Zaben 2023

Hakazalika akwai dukkan tsaffin shugaban kasa dake raye, tsaffin shugabannin Alkalai, shugaba majalisar dattawa Ahmad Lawan, Kakakin majalisar wakilai Femi Gbajabiamila, gwamnonin jihohin Najeriya 36 da kuma Antoni Janar na tarayya, Abubakar Malami.

Ku Cigaba Da Amfani Da Tsaffin Kudadenku, Zamu Bi Umurnin Kotun Koli: Gwamnatin Tarayya

Gabanin zaman, Antoni Janar na tarayya ta bayyana cewa za'a bi umurnin kotun koli na dakatad da shirin hana amfani da tsaffin takardun kudin Naira yau.

Abubuakar Malami ya ce ranar Laraba zasu koma kotu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel