APC da PDP Duk 1 ne: Jigon PDP Ya Share Atiku, Ya Fadi ‘Dan Takaransa a 2023

APC da PDP Duk 1 ne: Jigon PDP Ya Share Atiku, Ya Fadi ‘Dan Takaransa a 2023

  • Barista Julius Nnamani ya rabu da siyasar jam’iyya, ya ce yanzu ana duba mai neman takara ne
  • ‘Dan siyasar ba zai goyi bayan PDP ba, da alama zai zabi ‘dan takaran jam’iyyar LP ne a zaben 2023
  • Jigon na jam’iyyar PDP ya soki halin ‘yan siyasar yau, yake cewa APC da PDP duk sun zama daya

Abuja - Julius Nnamani wanda jagora ne a jam’iyyar hamayya ta PDP, ya ce Peter Obi mai neman mulki a LP ne kurum mafitan Najeriya a zaben 2023.

A wata hira da gidan talabijin yanar gizo ta Vanguard tayi da ‘dan siyasar, ya nuna cewa Peter Obi ne zai iya magance matsalar tulin bashin kasar nan.

Barista Julius Nnamani ya ce a duk cikin masu harin kujerar Muhammadu Buhari a zaben bana, ‘dan takaran jam’iyyar LP ne wanda ya fi kowa nagarta.

Kara karanta wannan

‘Dan Takarar Gwamna Ya Yi Hasashen Yadda Zaben Shugaban Kasa Zai Kasance a Kano

A tattaunawar da aka yi da shi, jagoran na jam’iyyar hamayya ta PDP ya shaidawa jaridar Vanguard cewa yanzu an tashi daga yin siyasar jam’iyya.

An daina bin Jam'iyya

A cewar Barista Nnamani, duk da su na jam’iyyar PDP, a zaben 2023 ana maganar wanda ya dace da shugabanci ne, ba jam’iyyar da mutum ya tsaya ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Dalilin Nnamani na fadan hakan shi ne yau an daina yin siyasar akida, an koma takara ido rufe, ya ce da Amurka ne da rokonsa za a rika yi ya yi takara.

"Yanzu babu maganar siyasar jam’iyya musamman a matakin jihohi domin cancantar mutum ce za tayi tasiri wajen zabensa ko rashin zabensa.
Saboda haka mutane za su duba cancanta ne kafin jam’iyyar siyasa wajen zaben ‘dan takara,
Jam’iyyun PDP da APC duk abu daya ne, an canza masu mulki ne kurum. Wasu ma za su karada duka jam’iyyun a shekara, duk daya suke.

Kara karanta wannan

Jam’iyyar APC ta Fitar da Matsaya a Kan Daga Zaben Shugaban kasa da ‘Yan Majalisa

Mutum daya ne kurum daga Kudu wanda ya cancanta idan aka duba irin abubuwan da ya yi, shi ne zai iya maganin bashin da ya adabe mu.
Mutumin da ya damka mulki da N75bn a asusun jihar da ba ta da mai a lokacin. Wannan ya nuna yadda ya fahimci ilmin tattalin arziki."

- Barista Julius Nnamani

NNPP za ta ci Kano

A wani rahoto da aka fitar, an ji Salihu Tanko Yakasai ya ba 'dan takaran NNPP, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso nasara a zaben Shugaban Kasa a Kano.

‘Dan takaran Gwamnan na Kano a jam’iyyar PRP ya na ganin Atiku Abubakar ne zai zo na biyu a 2023, sannan Bola Tinubu ya zo bayan NNPP da PDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel