Fashewar Bam A Masallaci Ya Kashe Mutum 59, Fiye Da 159 Sun Yi Munanan Rauni A Pakistan

Fashewar Bam A Masallaci Ya Kashe Mutum 59, Fiye Da 159 Sun Yi Munanan Rauni A Pakistan

  • An rasa rayyukan mutum 59 sannan wasu 159 sun jikkata sakamakon fashewar wani abu a masallacin Pakistan
  • Kawo yanzu ba bu wata kungiya da ta fito ta dauki nauyin kai harin amma wasu rahotanni na alakanta harin da Taliban
  • Imran Khan, tsohon Firai ministan Pakistan ya yi Allah wadai da harin, ya kuma yi ta'aziyya ga wadanda abin ya shafa

Pakistan - Wani fashewar abu da ake zargi bam ne a birin Peshawar, Pakistan, ya kashe a kalla mutane 59 ya kuma raunata wasu 157.

Rahotanni a ranar Litinin sun nuna cewa akwai alamu an saka bam din ne don halaka jami'an tsaro da ke kusa da masallacin wacce ke kusa da rukunin gidajen yan sanda.

Explosion
Fashewar Bam A Masallaci Ya Kashe Mutum 59, Fiye Da 159 Sun Yi Munanan Rauni A Pakistan. Hoto: @thecableng
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Hankula Sun Tashi A Gidan Magajiya Yayin Da Aka Tsinci Gawar Wata A Dakinta Na Otel

A cewar Dawn, wani kafar watsa labarai na kasar, jami'an yan sanda sun ce lamarin harin kunar bakin wake ne.

Bidiyo na CCTV da aka fitar daga bisani ya nuna wani mahari shi daya ya nufi masallacin a kafa dauke da pistol.

Rahoton ya kara da cewa maharin ya bude wa yan sanda da ke wajen shiga masallacin wuta kafin ya shiga ciki da gudu.

Daga nan ya bude wa wani mutum da ya yi kokarin taka masa birki wuta ya kuma shiga masallacin inda mutane suka taru don yin ibada, bayan nan abin fashewar ya fashe.

Martanin yan sanda

Riaz Meshood, kwamishinan yan sanda ya ce ana aikin ceton rai a cikin masallacin domin gini ya danne wasu.

Meshood ya ce:

"An saka dokar ta baci a asibitoci da ke birnin domin bawa wadanda abin ya shafa kulawa wadda ta dace."

Muhammad Khan, jami'in dan sanda, ya ce rufin masallacin ya rufta kasa bayan fashewar.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An kama ainihin mutanen da ke boye sabbin kudi, suna siyarwa a boye a Arewa

Ya kara da cewa ainihin cikin masallacin - wacce ke daukan mutum 200 zuwa 300 - ya rufta amma sauran ginin lafiyarsa kalau.

Bidiyo daban-daban a dandalin sada zumunta sun nuna yadda abin fashewar ya yi wa sassan masallacin illa.

Khan ya ce akwai yan sanda 300 zuwa 400 a yankin a lokacin da abin ya faru.

Babu wata kungiya da ta dauki nauyin kai harin, amma rahotanni sun danganta abin da kungiyar Taliban ta Pakistan.

Imran Khan, tsohon faraiministan Pakistan, ya yi ta'aziyya ya kuma ce an fara cikakken bincike.

A baya kun ji cewa wasu yan bindiga sun kai hari wani masallaci da ke garin Ughelli a jihar Delta, inda suka raunta masallata 11.

NAN ta rahoto cewa wani mazaunin garin ya ce lamarin ya faru misalin karfe 6.47 na safiyar a lokacin da al'umma ke sallar asubahi a masallacin da ke kan titin Okoroda a Ughelli.

Kara karanta wannan

Ikon Allah: Daga buya a kwantena, yaro ya farka daga bacci ya tsinci kansa a wata kasa

Asali: Legit.ng

Online view pixel