Hankula Sun Tashi A Gidan Magajiya Yayin Da Aka Tsinci Gawar Wata A Dakinta Na Otel

Hankula Sun Tashi A Gidan Magajiya Yayin Da Aka Tsinci Gawar Wata A Dakinta Na Otel

  • Mutanen wata unguwa a garin Onitsha da ke jihar Anambra sun tashi sun tarar da labari mara dadi bayan tsintar gawar wata budurwa
  • Rahotanni sun bayyana cewa masu shara ne suka tsinci gawar wata budurwa mai suna Chisom da ake ce yar gidan magajiya ce
  • Wasu na zargin wani kwastoma ne ya halaka ta yayin da wasu kuma suna ganin ba abin da ya faru ba kenan, yan sanda sun dauke gawarta kuma sun fara bincike

Onitsha, Anambra - An tsinci gawar wata mata yar gidan magajiya mai suna Chisom a dakinta a Otel da ke Onitsha a jihar Anambra.

Punch Metro ta tattaro cewa an tsinci gawar marigayiyar a ranar Litinin yayin da masu shara ke share dakinta.

Onitsha
Hankula Sun Tashi A Gidan Magajiya Yayin Da Aka Tsinci Gawar Wata A Dakinta Na Otel. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Fashewar Bam A Masallaci Ya Kashe Mutum 59, Fiye Da 159 Sun Yi Munanan Rauni A Pakistan

Lamarin ya janyo rudani a yankin a yayin da mazauna unguwa suka taru a wurin da abin ya faru suna tattaunawa.

Yayin da wasu ke zargin kashe ta aka yi, wasu na ganin ba abin da ya faru ba kenan.

Wata majiya, wacce ta ga gawar kafin a dauke ta kafin karfe 2.10 na ranar ta ce yanayin yadda ta ga gawar na nufin shake Chisom aka yi.

Wata majiyar kuma abokiyar aikin marigayiyar ta ce akwai yiwuwar kwastomanta na karshe da ta gani ne ya shake ta.

Ta ce marigayiyar ta yi hayaniya da wani kwastoma wanda a makon da ya wuce ya ce ya biya ta kudi amma ba ta biya masa bukata ba, kuma ya yi barazanar zai yi maganin ta.

Wata dattijuwa yar shekara 70 da ke kusa da otel din ta magantu tana mai cewa bata san dalilin da yasa ke kyale sauran abokin aikin suna tafiya ba yayin da aka tsinci gawar daya cikinsu.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Gwamnan CBN ya Dira Majalisar Tarayya, Ya Shiga Ganawa da Kakakin Majalisa

Yan sanda sun fara bincike kan mutuwar budurwar a otel

Yan sanda da suka ziyarci otel din daga Onitsha misalin karfe 12.30 na rana sun tafi tare da wasu ma'aikata, daga baya suka dawo.

Jim kadan, motar daukan marasa lafiya daga babban asibitin Onitsha ya taho ya dauki gawar.

DPO na yan sanda a Onitsha, Ifeanyi Ibru ya ce an fara bincike kan lamarin.

Ibru ya kara da cewa:

"Yan sanda sun san da batun kuma suna bincike; an dauke gawar."

Asali: Legit.ng

Online view pixel