Dalilin da Ya Sa Gwamnatin Burtaniya Ta Gayyaci Atiku, Majalisar Kamfen Dinsa Ta Magantu

Dalilin da Ya Sa Gwamnatin Burtaniya Ta Gayyaci Atiku, Majalisar Kamfen Dinsa Ta Magantu

  • Atiku Abubakar ya samu gayyata daga gwamnatin Burtaniya, an tattauna dashi kan wasu batutuwa
  • Jam'iyyar PDP ta fito ta yi bayani, ta bayyana gaskiyar abin da dan takarar na PDP ya tattauna da Burtaniya
  • Hakazalika, PDP ta ce akwai haske ga Atiku a zaben shugaban kasa da za a yi nan da wata guda a Najeriya

Najeriya - Majalisar kamfen din takarar shugaban kasa ta jam'iyyar PDP ta bayyana dalilin da yasa gwamnatin kasar Burtaniya ta gayyaci Atiku don tattaunawa dashi, New Telegraph ta ruwaito.

A cewar majalisar, an gayyaci Atiku ne domin tattauna batutuwan da suka shafi gamayya da hadin gwiwa tsakanin Najeriya da Burtaniya a nan gaba idan ya gaji Buhari.

Wannan na fitowa ne daga daraktan yada labaran majalisar, Otunba Dele Momodu a cikin wani sako da ya bayar a jiya Talata 10 ga watan Janairu.

Dalilin da yasa Burtaniya ta gayyaci Atiku don tattaunawa dashi
Dalilin da Ya Sa Gwamnatin Burtaniya Ta Gayyaci Atiku, Majalisar Kamfen Dinsa Ta Magantu | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Akwai yiwuwar Atiku ya lashe zabe, inji Dele Momodu

Momodu ya kuma bayyana cewa, akwai haske mai kyau game da nasarar Atiku a zaben da za a gudanar a cikin watan Fabrairu mai zuwa, rahoton Vanguard.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar sakon nasa:

"Majiya ciki ta naqalto cewa, zaben ciki gida a na gwamnatin Burtaniya ya nuna AA (Atiku Abubakar) ne dan takarar da kan gaba kuma akwai yiwuwar aiki kafada-kafada dashi don amfanin kasashen biyu.
"Wannan na da matukar muhimmanci domin Burtaniya na son habakawa da fadada alakar kasuwanci da Najeriya."

Rikicin da ke gaban Atiku a matakin jam'iyya

Duk da wannan, har yanzu dan takarar na shugaban kasa a PDP na ci gaba da fuskantar barazana da koma baya a jam'iyyar, kasancewar akwai wasu jiga-jigan jam'iyyar da ke adawa dashi.

Gamayyar gwamnonin G-5 na ci gaba da nuna adawa da shugabancin PDP a matakin kasa, kana sun ce babu ruwansu da Atiku.

Gwamnonin dai burinsu shine; su ga an tsige Ayu Iyorchia ammatsayin shugaban jam'iyyar na kasa tare da ba wani dan yankin Kudu.

Burtaniya ba za ta tsoma baki a zaben bana ba

A tun farko kun ji cewa, kasar Burtaniya ta ce ba za ta sanya baki a zaben da za a gudanar a Najeriya ba kwata-kwata.

Wannan na fitowa ne daga bakin Ms Catriona Laing, babbar kwamishiniyar Burtaniya a Najeriya lokacin da take magana game da zaben na bana.

Ta kuma bayyana cewa, kasar ta Turai za ta tsaya ne tsaka-tsaki kan dukkan abubuwan da za su faru a zaben.

Asali: Legit.ng

Online view pixel