Kyakkyawan Karshe: Malamar Makaranta Ta Mutu Tana Tsaka Da Karatun Al-Qur'ani

Kyakkyawan Karshe: Malamar Makaranta Ta Mutu Tana Tsaka Da Karatun Al-Qur'ani

  • Malama ta hadu da mahalaccinta tana tsaka da karatun Al-Qur'ani a dakin taro a kasar Indonesia
  • Bidiyon da ya yadu a soshiyal midiya ya nuna yadda matar ta fadi yayinda take karata Aya ta 163 na Suratul Baqara
  • Kasar Indonesia ce kasar da ta fi yawan mabiya addinin Islama a fadin duniya

Bidiyon wata malamar makaranta yar kasar Indonesia wacce ta rasu tana karatun Al-Qur'ani mai girma ya bayyana a kafafen ra'ayi da sada zumunta na yanar gizo.

Bidiyon da aka dauka yayin wani taron addinin Musulunci ya nuna yadda Malamar ke karanta Suratul Baqara.

Bidiyon mai tsawon minti 1:29 ya nuna yadda ta fadi tana tsaka da karatun ta 163 na Suratul Baqarah.

Tana gab da faduwa tayi tsallake zuwa aya mai ce "Ku sani Ubangijinku Daya ne".

Kara karanta wannan

Taron Gangamin UN: Hotunan Da Bidiyon Shugaba Buhari Yayinda Ya Isa Birnin New York Cikin Dare

Yayinda Likitoci suka duba ta, sun sanar da cewa ta rigami gidan gaskiya.

Kalli bidiyion da @muslimdaily_ ta daura:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Daukacin mabiyanmu sun yi mata addu'a

Isah Muhammad yace:

"Allah Ya jikanta da rahama
Mukuma Allah Ya qyautata namu qarshen Bayan nasu
Don albarkan manzon Allah"

Rashida Bala yace:

"Masha Allah irin mutuwar da akeso kenan Allah yasa muyi kekkyawan qarshe ita Kuma Allah yasa annabi s a w ya karb'i baqoncin ta."

Muhammad Auwal Usman Tal'udu yace:

"Allah ya gafarta mata muma Allah yasa muyi karshe mai kyau ameen y Allah."

Amir M. Aboki:

"Allah Akbar Masha Allah! Allah ya ji qan ta yai ma ta Rahmah, in na mu ya zo Allah ya sa mu cika da Iman."

Jamilu Sale:

"Allahu Subhanahu Wata'ala Ya Kai rahama kabarin ta hada damu intamu tazo da Iyayammu gabadaya da ahalimmu da musulmai.

Kara karanta wannan

Aminu Daurawa: Shawarwari 5 Da Na Ba Ummita Kafin Mutumin China ya kashe ta

Ya Ubanginjin Al-Arshi Mai tsarki da girma."

Asali: Legit.ng

Online view pixel