Kisan Ummita: An Gurfanar da ‘Dan Chana, Kotu ta Yanke Hukuncin Farko

Kisan Ummita: An Gurfanar da ‘Dan Chana, Kotu ta Yanke Hukuncin Farko

  • Kotu ta bayar da umurnin tsare mutumin kasar China, Geng Quanrong, wanda ake zargi da kisan budurwarsa yar Kano, Ummita Buhari
  • Mai shari'a a kotun majistaren, Hanif Sanusi Ciroma, ya ce basu da hurumin sauraron wannan shari'ar
  • Sai dai ya bayar da umurnin tsare Mista Geng a magarkamar Kurmawa zuwa lokacin da za a gurfanar da shi a gaban kotun sama

Kano - Wata kotun Majistare da ke zama a kotu ta yi umurnin garkame ‘dan kasar China, Geng Quanrong, kan kisan masoyiyarsa yar Najeriya, Ummukulsum Sani Buhari.

Kotun ta yi umurnin tsare wanda ake zargin a gidan gyara hali na Kurmawa, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Umurnin kotun ya biyo bayan gurfanar da wanda ake zargin da yan sanda suka yi a gaban kotun kan tuhumar aikata kisan kai wanda yayi karo da sashi na 221 na Kundin Pinal Kod.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotu Ta Raba Gardama Tsakanin FG da ASUU, Ta Yanke Hukunci Kan Yajin Aiki

Ummita
Kisan Ummita: An Gurfanar da ‘Dan Chana, Kotu ta Yanke Hukuncin Farko Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Sai dai kuma, mai shari’a, Hanif Sanusi Ciroma, ya bayyana cewa kotun bata da hurumin sauraron shari’ar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga bisani, lauyan masu kara, Khalifa Auwal Hashim, ya roki kotun da ta dawo da wanda ake zargin zuwa magarkama kafin lokacin da caji zai fito don gurfanar da shi tunda bata da hurumin gudanar da shari’a, Aminiya ta rahoto.

Da take amsa rokon, mai shari’ar ta zartar da hukunci cewa a tsare wanda ake zargin a gidan gyara hali har zuwa ranar 13 ga watan Oktoba, don gurfanar da shi a gaban kotun da ke da ikon sauraron shari’ar.

Aika-Aikar Dan China: Gwamnatina Za Ta Dauki Mataki Kan Makashin Ummita, Inji Ganduje

A baya mun ji cewa gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ta sha alwashin tabbatar da ganin doka ta yi aikinta a kan lamarin kisan Ummukhulthum Sani Buhari, da ake zargin wani dan kasar China da yi.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Majalisar Dattawa Ta Fara Tantance Mukaddashin Alkalin Alkalan Najeriya

Da yake jawabi kan lamarin a gidan gwamnatin jihar, Ganduje ya ce dole maganar shari’a ta shigo ciki kuma sai doka ta yi aikinta tunda har abun ya danganci zubar da jini ne, sashin Hausa na BBC ta rahoto.

Gwamnan ya kuma bayyana cewa tuni suka sa aka tsare wanda ake zargin mai suna Mista Geng Quanrong, bayan jama’a sun kama shi a gidan iyayen marigayiyar a ranar Juma’ar da ta gabata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel