Kasashe 10 mafi karfin tattalin arziki a Nahiyar afrika ta ukun za ta baku mamaki

Kasashe 10 mafi karfin tattalin arziki a Nahiyar afrika ta ukun za ta baku mamaki

- Nahiyar Afrika yanki ne da yake da albarkatu da dama wadanda suka hada albarkatun da ke cikin karkashin kasa, danyen mai, da kuma hada-hadar kudi da ta kasuwanci. Sai dai abin mamaki Kasar Najeriya ba ita ce kasa da ta zo ta farko ba duk da cewar ana ganin kasar ita ce mafi karfin arziki a Afrika, amma hakan ba zai rasa nasaba da faduwar farashin danyen man fetur a yan skearun baya a kasuwar duniya ba.

Kasashe 10 mafi karfin tattalin arziki a Nahiyar afrika ta ukun za ta baku mamaki
Africa

Ga jerin jadawalin kasashen da kuma kimar kudin da suke da shi:

1. South Africa (GDP: $595.7 billion)

Kasashe 10 mafi karfin tattalin arziki a Nahiyar afrika ta ukun za ta baku mamaki
South Africa

Wannan kasa, kasa ce da ta yi fice wajen samun albarkatun cikin karkashin kasa da suka hada zinare, azurfa, Tagulla, da duk wasu ma'adanai dake cikin karkashin kasa. Kuma kasa ce da ke da manyan birane har guda biyu; wato Johannesburg da kuma Cape Town, wadanda kowa yake burin zuwa idan ya ziyarci kasar, hakan yana taimakawa kasar wajen samun kudin shiga.

2. Egypt (GDP: $551.4 billion)

Kasashe 10 mafi karfin tattalin arziki a Nahiyar afrika ta ukun za ta baku mamaki
Egypt

Kasar Egypt kasa ce da ta yi fice wajen cigaba wanda ya shafi fasahar dan adam, wannan cigaba nasu ya samo asali ne tun a shekara ta 3200 tun kafin haihuwar annabi Isah (A. S). Kuma kasa ce da take da tsaunuka, manyan gina-gine da sauran wajen shakatawa da yawon bude ido a wata hanyar karin samun kudaden shiga.

3. Nigeria (GDP: $478.5 billion)

Kasashe 10 mafi karfin tattalin arziki a Nahiyar afrika ta ukun za ta baku mamaki
Nigeria

Najeriya ita ce kasa mafi shahara a Nahiyar Afrika, musamman idan aka yi duba da irin kamfanoni da take da su, da kuma arzikin man fetur da Allah ya albarkace kasar da shi. Kasa ce da take dauke da adadin mutanen da sun kai Miliyan 180 kuma ana sa ran zata iya zama ta 20 a jerin kasashen duniya mafi bunkasar arziki, musamman idan aka yi duba da birane irin su Legas dake dauke da manyan gine- gine da kuma hada-hadar kudi da ake gudanarwa.

KU KARANTA: Mutane 3 masu tsananin taurin kai da kunnan kashi a Gwamnatin Buhari

4. Algeria (GDP: $284.7 billion)

Kasashe 10 mafi karfin tattalin arziki a Nahiyar afrika ta ukun za ta baku mamaki
Algeria

Wannan kasa, ita ma kamar sauran kasashe tana da albarkatun kasa da dama sai dai arzikinta ya fi yawa ta bangaren man fetur da kuma gas, wanda ta nan ta fi samun kudin shiga sosai.

5. Morocco (GDP: $180 billion)

Kasashe 10 mafi karfin tattalin arziki a Nahiyar afrika ta ukun za ta baku mamaki
Morocco

Wannan kasa ta Morocco ta yi fice sosai a yanki Arewan Afrika musamman ta bangaren abinda ya shafi noma, harkar saka, sadarwa da kuma yawon bude ido, wadannan abubuwa sun taimaki kasar matuka gaya wajen bunkasar tattalin arzikinta.

6. Angola (GDP: $131.8 billion)

Kasashe 10 mafi karfin tattalin arziki a Nahiyar afrika ta ukun za ta baku mamaki
Angola

Zai zama abin mamaki ga duk wanda ya ga kasar Angola a cikin jerin kasashen da suka fi arziki a Nahiyar Afrika, amma ba abin mamaki bane idan aka yi duba da irin yadda suka maida hankalinsu akan harkar danyen man fetur, gas, da kuma hakar Gwal daga karkashin kasa, duk da cewa har yanzu tana farfadowa ne daga yakin basasar da ta tsinci kanta ne tun shekaru 27 da suka wuce.

7. Ethiopia (GDP: $118.2 billion)

Kasashe 10 mafi karfin tattalin arziki a Nahiyar afrika ta ukun za ta baku mamaki
Ethiopia

Wannan kasa tattakin arzikinta ya yi matukar habaka a cikin kankanin lokaci saboda yadda matasan garin suka maida hankali akan Noma, amma da yawan wannan matasan na kasar ba su cika zama a manyan biranen kasar ba sun fi zama inda zasu fi maida hankali ne akan abinda ya shafi harkarsu ta noma, sauran dake babban birnin kasar sun fi yin abinda ya shafi harkar sadarwa da sauransu.

8. Tunisia (GDP: $108.4 billion)

Kasashe 10 mafi karfin tattalin arziki a Nahiyar afrika ta ukun za ta baku mamaki
Tunisia

Man fetur, yawon bude ido da sarrafa kayan motoci da shi kasar ta yi fice ta wannan bangare. Kasa ce mai arziki musamman idan ka yi duba da biranen dake garin kamar irin babban birnin kasar wato Tunis wanda yake dauke da abubuwan more rayuwa.

9. Ghana (GDP: $90.41 billion)

Kasashe 10 mafi karfin tattalin arziki a Nahiyar afrika ta ukun za ta baku mamaki
Kasashe 10 mafi karfin tattalin arziki a Nahiyar afrika ta ukun za ta baku mamaki

Ita kuwa a iya cewa kasa ce da ta dogara da kanta ta bangaren fasaha da abubuwan cigaban rayuwa. Wasu birane na garin kamar su Accra da Kumasi da sun fi yin shura ne ta bangaren abinda ya shafi harkar masana'antu, wanda hakan yasa duk wanda zai yi kasuwanci da kasar Ghana yake jin dadin mu'amala.

10. Sudan (GDP: $89.97 billion)

Kasashe 10 mafi karfin tattalin arziki a Nahiyar afrika ta ukun za ta baku mamaki
Sudan

Kasar Sudan ita ce kasa ta karshe a jerin wannan kasashe, ita ma kamar sauran tana da albarkar man fetur kamar sauran kasashe amma hakan bai hana ta bunkasa tattalin arzikinta ta bangaren Noma ba, kasar ta yi shuhura sosai musamman idan aka yi duba da yadda man fetur ke taimakon arzikin kasar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng