Mabaraci Ya Tsallake Rijiya Da Baya Yayinda Aka Kamashi Kudi N500,000 a jihar Legas

Mabaraci Ya Tsallake Rijiya Da Baya Yayinda Aka Kamashi Kudi N500,000 a jihar Legas

  • Wasu matasa sun damke wani mabaraci a jihar Legas da makudan kudi sama da rabin miliyan
  • Bayan haka an ga kullin magungunan da layu wanda hakan yasa aka fara zargin mutumin
  • Ba tsamannni matasan suka far masa zasu lakada masa duka kafin wani babban a nguwa ya ceceshi

Hankulan jama'a sun tashi a unguwar Arilesola dake Abule Egba, jihar Legas ranar Laraba bayan damke wani mabaraci da guru da layu da kuma kudi N500,000.

Ana cikin hayaniyar mazauna unguwar suka taru wajen don ganewa idonsu.

Mabaracin mai suna Festus Dia ya nemi barar N50 hannun wasu mutane kuma yaki amsan duk kudin da ba N50 ba.

Hakikancewarsa kan cewa N50 yake so ya tada hankalin jama'a inda suka fara bincikensa.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Wata cuta ta kama kama Nnamdi Kanu a hannun DSS, inji lauyansa

Yayinda suka binciki jikinsa, sun tarar da N500,000, wasu guru da layu, da kuma Goro.

Kai tsaye matasan suka far wa mutumin sukayi kokarin hallakasa kafin mai unguwar ya hanasu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mabaraci
Mabaraci Ya Tsallake Rijiya Da Baya Yayinda Aka Kamashi Kudi N500,000 a jihar Legas Hoto: TheNation
Asali: Facebook

TheNation ta ruwaito cewa mabaracin yayi bayanin cewa shi dan jihar Ondo ne kuma yana bara ne don kula da 'yayansa 10.

Yace hakazalika yana sana'ar sayar da barasa.

A cewarsa:

"Suna na Festus Dia, Ni dan kabilar Ijaw ne a jihar Ondo kuma ni mazaunin Ekoro ne a Abule Egba, kwana na 8 kacal a unguwar."
"Kayan barasa nake sayarwa kuma ina bara. Ina bara ne don samun kudin jari."
"Maganin da aka gani kuma na kariya ne. Yau N4,800 kacal na samu wajen bara."

Wani Mutum Ya Nuna Hotunan Layyu Da Guraye Masu Ban Tsoro Da Ya Tono A Gidan Haya Da Ya Shiga A Legas

Kara karanta wannan

Gwamna Soludo ya Wanke Fulani, Ya Bayyana Wadanda ke Assasa Rashin Tsaro a Anambra

A wani labarin kuwa, wani mutum dan Najeriya ya bada labarin abin ban tsoro da ya yi karo da shi bayan ya kama hayan gida a Jihar Legas.

Matashin mai suna Elkros a Twitter ya ce ya biya hayan wani gida amma tayil din bai masa ba.

Don haka sai ya yanke shawarar fasa tayil din gidan domin a sake masa sabbi. Yayin aikin, ma'aikatan sun gano layyu da guraye da aka binne a karkashin tayil din.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel