Ahmad Yusuf
10081 articles published since 01 Mar 2021
10081 articles published since 01 Mar 2021
Majalisar dattawa da majalisar wakilan tarayya sun haɗu sun amince da makudan kuɗin da shugaban ƙasa Tinubu ya nemi kara wa a kasafin kuɗin 2023.
Tsageru ɗauke.da muggan makamai sun kai farmaki har cikin gida, sun yi awon gaba da shugaban ma'aikatan shugaban majalisar dokokin jihar Adamawa.
Wasu masu zanga-zanga sun yi tattaki har zuwa zauren majalisar tarayya da ke Abuja ranar Laraba, sun buƙaci a tsige Bello Matawalle daga matsayin ministan tsaro.
Mambobin ƙungiyar gwamnonin babbar jam'iyyar adawa ta ƙasa PDP karkashin jagorancin Gwamna Bala Muhammed na Bauchi sun shiga ganawa da ministan Abuja.
Majalisar dattijan Najeriya ta tantance tare da tabbatar da naɗim sabbin kwamishinonin hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC a zaman yau Laraba.
Rahotanni sun bayyana cewa ana zaman makokin kisan matasa 17 da Boko Haram ta yi a jihar Yobe, wank ya sake tashi da masu zuwa jana'iza, an rasa rayuka 20.
Babbar Kotun tarayya mai zama a Abuja ta gindaya wa tsohon gwamnan babban bankin Najeriya wa'adin kawo kansa gabanta kan wasu makudan kuɗi da aka ciyo bashi.
Gwamnatin tarayya ta baiwa ɗaliban jami'ar Gusau da aka ceto tallafin kuɗi sama da Naira dubu ɗari biyu, in ji gwamnatin jihar Zamfara a wata sanarwa.
Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta zargi gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, da kulla harin da aka yi yunkurin halaka ta a lokacin zaben da ya gabata.
Ahmad Yusuf
Samu kari