Kotun Ɗaukaka Kara Ta Kwace Kujerar Ɗan Majalisar Tarayya Na PDP a Arewa, Ta Bada Umarni

Kotun Ɗaukaka Kara Ta Kwace Kujerar Ɗan Majalisar Tarayya Na PDP a Arewa, Ta Bada Umarni

  • Kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da hukuncin ƙaramar Kotu wanda ya ayyana zaben ɗan majalisar Birnin Kudu/Buji a matsayin wanda bai kammalu ba
  • A zaman yanke hukunci, Kotun ta umarci hukumar zaɓe ta ƙasa INEC ta shirya sabon zaɓe a rumfuna 8 cikin kwanaki 30
  • Tun da fari dai INEC ta ayyana Adamu Yakubu na PDP a matsayin wanda ya ci zaɓe amma ɗan takarar APC ya garzaya Kotu

Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Kotun ɗaukaka ƙara mai zama a birnin tarayya Abuja ta kara tabbatar da hukuncin da Ƙotun zaɓe ta yanke kan kujerar ɗan majalisa tarayya mai wakiltar Birnin Kudu/ Buji.

A rahoton da jaridar Daily Trust ta ruwaito, Kotun ɗaukaka kara ta tabbatar da hukuncin ƙaramar Kotu wanda ya ayyana zaɓen mazaɓar da wanda bai kammalu ba.

Kara karanta wannan

Abba vs Gawuna: Kotun daukaka kara ta sanya ranar fara sauraron shari'ar gwamnan Kano

Kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da hukuncin Kotun zaɓe.
Kotun Daukaka Kara Ta Kara Kwace Kujerar Ɗan Majalisar Arewa, Ta Umarci INEC Hoto: HouseNGR
Asali: Facebook

Da yake yanke hukunci, shugaban kwamitin Kotun mai shari'a Ogochuku Anthony Ogakwu, ya umarci hukumar zaɓe INEC ta shirya ƙarishen zaɓe a akwatu 8 cikin wata ɗaya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotun ta yanke wannan hukunci ne a ƙarar da ɗan takarar People Democratic Party (PDP), Honorabul Adamu Yakubu, ya ɗaukaka a gabanta.

Yadda aka fafata shari'a tun farko

Tun da farko, INEC ta ayyana ɗan takarar na jam'iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaɓen ɗan majalisa mai wakiltar Birnin Kudu/Buji a majalisar wakilan tarayya.

Sai dai babban abokin hamayyarsa Magaji Dau Aliyu na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ya kalubalanci sakamakon da INEC ta bayyana.

Kotun sauraron karar zaɓe mai zama a Dutse, babban birnin jihar Jigawa, ta ayyana sakamakon zaben 2023 na mazabar Birnin Kudu/Buji a matsayin wanda bai kammala ba.

Kara karanta wannan

APC da LP sun gamu da cikas, Kotun ɗaukaka ƙara ta yanke hukunci kan nasarar 'yan majalisar tarayya 2

Amma Honorabul Yakubu ya garzaya Kotun ɗaukaka ƙara kuma duk da haka hukuncin bai masa daɗi ba.

A halin yanzu, INEC zata shirya sabon zaɓe a rumfuna takawas wanda jimulla su ke da masu kaɗa kuri'a 6, 351, ɗan takarar APC na bin ɗan majalisa da tazarar ƙuri'u 1,926.

Wani malamin makaranta kuma mazaunin Birnin Kudu, Aminu Majeh, ga shaida wa Legit Hausa cewa ba ya tunanin APC zata kai labari koda an sake zaɓen.

A cewarsa, PDP ta shiga gaban APC da kuri'u kusan 2000 amma ya ce a yanzu jama'ar Birnin Kudu da Buji sun fi son Magaji Dau na APC.

"Ko da an sake zaben PDP ta riga ta ba APC tazarar kusan kuri'u 2000 kaga kwace kujerar nan abu ne mai wuya."
"Amma maganar gaskia a yanzu anfi son Magaji Dau Aliyu na APC ga samu nasara saboda korafi yayi yawa cewa shi Dan Maliki ba shi da kyauta."

Kara karanta wannan

Kotun ɗaukaka ƙara ta raba gardama, ta yanke hukunci kan nasarar ɗan majalisar tarayya daga Kaduna

NASS ta amince da ƙarin ƙasafin 2023

A wani rahoton na daban Majalisun tarayya sun amince da buƙatar shugaba Bola Tinubu na kara N2.17tr a kasafin kuɗin 2023 karo na biyu kenan.

Wannan mataki ya biyu bayan tsallake karatu na uku da kasafin ya yi da kuma aminta da rahoton zaman haɗin guiwa na majalisun biyu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel