Dalilin da yasa Jami'anmu suka kama Shugaban KASUPDA - EFCC
- Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta yi martani kan dalilin da yasa jami'anta suka kama Shugaban hukumar KASUPDA, Ismail Umaru Dikko
- Kakakin hukumar ta EFCC, Wilson Uwujaren, ya bayyana cewa an gayyaci Dikko ne saboda wasu lamura da suka shafi ka’ idar aiki ba wai don zamba ba
- Ya kuma bayyana cewa sun warware batun da ya kai ga kamun na Dikko wanda bai fayyace ko menene ba
Kaduna - Hukumar yaki da cin hanci da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa(EFCC), ta ce jami'anta sun cafke Darakta Janar na Hukumar Raya Biranen Jihar Kaduna (KASUPDA), Ismail Umaru Dikko, kan wasu al'amura na hukumar.
Rahotanni sun kawo cewa jami’an hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa, a safiyar ranar Litinin, 11 ga watan Oktoba, sun mamaye hedkwatar KASUPDA tare da dauke Dikko a cikin wata bakar mota kirar Hilux Toyota zuwa ofishinsu na Kaduna.
KASUPDA ce hukumar da ke kula da cigaba da tsare-tsaren gine-gine a biranen jihar Kaduna. Wannan hukuma ta yi suna wajen rusa gine-gine a Kaduna.
Daily Trust ta ruwaito cewa mai magana da yawun hukumar, Wilson Uwujaren, ya bayyana cewa ba wai an gayyaci Dikko don zamba bane illa saboda wasu lamura da suka shafi ka’ idar aiki.
Kakakin na EFCC, wanda bai yi karin bayani kan batutuwan da suka shafi dokar ba, ya bayyana cewa an magance matsalolin da ya kai ga kamun Dikko.
Jaridar ta nakalto Uwujaren yana cewa:
"An gayyace shi ne ba don zamba ba illa saboda wasu lamura da suka shafi ka’ idar aiki tare da hukumarsa wacce aka warware."
Sai dai kuma, wani babban jami’i a hedikwatar EFCC ya shaida wa jaridar cewa akwai akalla kararraki guda biyar gaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa a kan KASUPDA da shugabanta.
Jami'in, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya yi bayanin cewa masu karar sun yi zargin cewa an sayar da mafi yawan filayen da aka kwato bayan rushe su, ga wasu kusoshi da mutanen da ke biyayya ga gwamnatin jihar Kaduna.
Ya kara da cewa jami'an sun kama shugaban ne saboda kin amsa gayyatar da aka yi masa sau uku domin karin haske kan zargin.
Jami’an EFCC sun dura ofishin KASUPDA, sun yi gaba da Shugaban Hukuma
A baya mun kawo cewa wasu jami’an EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa, sun shiga hedikwatar hukumar KASUPDA da ke garin Kaduna.
Jaridar Daily Trust tace a safiyar Litinin, 11 ga watan Oktoba, 2021, aka ga ma’aikatan EFCC a hukumar KASUPDA, inda suka yi gaba da Darekta Janar.
Rahotanni sun ce EFCC tayi ram da shugaban hukumar, Malam Ismail Umaru Dikko. Zuwa yanzu babu wanda ya san laifin da ake zargin Dikko da aikata wa.
Asali: Legit.ng