Yanzu nan: Jami’an EFCC sun dura ofishin KASUPDA, sun yi gaba da Shugaban Hukuma

Yanzu nan: Jami’an EFCC sun dura ofishin KASUPDA, sun yi gaba da Shugaban Hukuma

  • Wasu jami’an hukumar EFCC sun shiga hedikwatar KASUPDA a safiyar Litinin
  • Ma’aikatan EFCC sun tasa keyar, Malam Ismail Umaru Dikko, sun yi gaba da shi
  • An yi gaba da shugaban hukumar yayin da yake yin taro a ofis da ma’aikatansa

Kaduna - Wasu jami’an EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa, sun shiga hedikwatar hukumar KASUPDA da ke garin Kaduna.

Jaridar Daily Trust tace a safiyar Litinin, 11 ga watan Oktoba, 2021, aka ga ma’aikatan EFCC a hukumar KASUPDA, inda suka yi gaba da Darekta Janar.

Rahotanni sun ce EFCC tayi ram da shugaban hukumar, Malam Ismail Umaru Dikko. Zuwa yanzu babu wanda ya san laifin da ake zargin Dikko da aikata wa.

Wata majiya a ma’aikatar tace Dikko yana cikin gana wa da ma’aikatansa ne jami’an EFCC su ka shigo ofis, suka ta fi da shi cikin wata motar Toyota Hilux.

Kara karanta wannan

Babu maganar wahalar man fetur, kungiyar NUPENG ta fasa tafiya yajin-aiki a yau

Babban ofishin KASUPDA
Hukumar KASUPDA ta Kaduna Hoto: kasupda.kdsg.gov.ng
Asali: UGC

Yadda aka yi ram da KASUPDA-DG

An samu ‘yar takaddama tsakanin ma’aikatan hukumar jihar ta KASUPDA da wadannan jami’an EFCC biyu da suka zo dauke da bindigogi a cikin motarsu.

Ma’aikatan KASUPDA sun yi yunkurin hana ma’aikatan EFCC tafiya da shugaban na su. Daga baya Malam Dikko ya umarce su da su bude kofa, a tafi da shi.

Wannan lamari ya auku ne da kimanin karfe 10:00 na safe. Ana zargin cewa yanzu haka Dikko yana babban ofishin EFCC na shiyyar Arewa maso yamma.

Ismail Umaru Dikko

Tun 2019 gwamna Nasir El-Rufai ya nada Malam Ismail Umaru Dikko a matsayin Darekta Janar na KASUPDA. Kafin nan yana cikin masu ba gwamna shawara.

KASUPDA ce hukumar da ke kula da cigaba da tsare-tsaren gine-gine a biranen jihar Kaduna. Wannan hukuma ta yi suna wajen rusa gine-gine a Kaduna.

Kara karanta wannan

2023: Tsohon dan takarar shugaban kasa ya koma APC a hukumance, ya gana da shugaban jam'iyyar a Abuja

Manema labarai sun ce tun tuni EFCC ta aika wa Ismail Dikko gayyata, amma ya ki amsa kiransu. Hakan ta sa wannan karo, aka zo aka dauke shi da karfi, da yaji.

Tsohuwar Sarki Abba ta cika

Dazu aka ji cewa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya aika wa Sarki Abba, da mutane da gwamnatin Adamawa ta’aziyyar rashin Hajiya Aishatu Abba.

Malam Garba Shehu ya ce shugaba Buhari ya tura wakilai wajen jana’izar Hajiya Aishatu Abba, tun da bai samu zuwa garin Yola inda aka yi mata jana'iza ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel