Maƙwabci na ya damfare ni N1,000,000, Magidanci ya yi ƙara a kotu

Maƙwabci na ya damfare ni N1,000,000, Magidanci ya yi ƙara a kotu

  • Wani dan kasuwa, Vincent Okam ya bayyana yadda makwabcin sa James Ibe ya tafka ma sa damfara
  • Ya bayyana wa wata kotu dake Kubwa a Abuja hakan a ranar Laraba hakan, inda ya ce ya ci amanar sa
  • A cewar sa bayan Ibe ya ranci kudin sa daga baya ya ba shi takardar banki ta bogi don ya je ya ciri kudi

FCT, Abuja - A ranar Alhamis, wani dan kasuwa mai shekaru 41, Vincent Okam ya sanar da kotu mai daraja 1 da ke Kubwa a Abuja cewa tsohon makwabcin sa, James Ibe ya damfare shi N1,000,000.

‘Yan sandan Jabi da ke Abuja sun kama Ibe da cin amana bisa ruwayar Daily Nigerian.

Maƙwabci na ya damfare ni N1,000,000, Magidanci ya yi kara a kotu
Maƙwabci na ya damfare ni N1,000,000, Magidanci ya yi kara a kotu. Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Femi Adesina: Ya dace a ce Sanata Abaribe ya na can ya na shakawata a gidan fursuna

Yayin da dan sanda mai gabatar da kara, Babajide Olanipekun ya rako shi, Okam ya bayyana cewa makwabcin sa na Kubwa ta gabace shi don ya ara ma sa N1,000,000 a 2014.

Har dalleliyar mota ya siya wa matarsa amma ya hana ni kudi na

Kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito, ya bayyana cewa:

“Ya yi alkawarin biya na bayan wata daya da na ba shi. Bayan makonni 2 ya kira ni don mu tattauna ashe duk salon damfara ne.
“Yayin tattaunawar, ya ce zai biya ni har da ribar kashi 5 bisa dari na kudin da na ba shi don ya yi sana’a.
“Bayan wata daya, ya kawo min takardar banki amma da na je da ita sai banki su ka tabbatar min ta bogi ce kuma babu kudi a asusun sa.
“Bayan na fuskance shi sai ya yi alkawarin zai biya ni amma har yau bai biya ni ba. Har na tashi daga Kubwa, tun daga nan ban samun damar ganin sa.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta mayar da yara 360,000 da basa zuwa makaranta zuwa ajujuwa a Katsina

“Ya bani takardar banki wacce ya rubuta zan amshi N1,100,000 bayan watanni 6, daga nan na ce bana bukatar takarda ni kudi nake so.
“Har ce min yayi ya yi tafiya don wata sana’a.
“Na lura har mota kirar Toyota Camry ya siya wa matarsa kuma na bukaci kudi na amma ya ce ba ya da su.”

Alkalin kotun, Muhammad Adamu ya daga karar zuwa ranar 11 ga watan Nuwamba don a kammala bincike akan lamarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel