Femi Adesina: Ya dace a ce Sanata Abaribe ya na can ya na shakawata a gidan fursuna

Femi Adesina: Ya dace a ce Sanata Abaribe ya na can ya na shakawata a gidan fursuna

  • Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman, Femi Adesina, ya ce kamata yayi Sanata Abaribe na gidan kurkuku yanzu haka
  • Ya sanar da hakan ne a wata takarda inda ya yi wa sanatan shagube duk da bai kira sunansa kai tsaye ba yayin maganganun
  • Adesina ya ce sanatan na amfani da miyagun kalamai wurin tada zaune tsaye, sai dai shugaban kasa daidai ya ke da shi tare da mukarrabansa

Femi Adesina, mai bada shawara na mausamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai, ya ce ya dace a ce Sanata Eyinnaya Abaribe ya na can ya na shakatawa a gidan fursuna, Daily Trust ta wallafa.

Abaribe, dan jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP kuma sanata daga jihar Abia, ya taba tsaya wa Nnamdi Kanu, shugaban 'yan a waren IPOB a kotu kafin ya tsallake beli ya bar kasar a 2017.

Kara karanta wannan

2023: Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Moghalu ya fice daga jam'iyyar YPP ya koma sabuwar jam'iyya

Femi Adesina: Ya dace a ce Sanata Abaribe ya na can ya na shakawata a gidan fursuna
Femi Adesina: Ya dace a ce Sanata Abaribe ya na can ya na shakawata a gidan fursuna. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Daga bisani an cafke Kanu kuma a halin yanzu ya na nan tsare hannun jami'an tsaron farin kaya, DSS, Daily Trust ta ruwaito.

A takardar da ya fitar ta makon nan, Adesina ya yi shagube kan yadda Abaribe ya tsaya wa Kanu a kotu har ya samu beli. Duk da bai taba kiran Abaribe ko Kanu ba, a bayyane yake da su biyun ya ke maganar.

"Wasu mutane suna tada hankula ta kalamansu da ayyukansu, hakan ke kara habaka kalubalen tsaron da mu ke fama da shi. Sai ka dinga tantamar daga ina suke kuma me yasa suke kara banka mana wutar.
“Akwai wani sanata mai abun dariya wanda ke maganganu kan abubuwa a kasar nan kuma ya na amfani da kalamai marasa dadi ga shugabanni.

Kara karanta wannan

2023: Jigon APC da ya shiga gidan yari ya fito, yana maganar neman Shugaban kasa

“Ya tsaya wa wani wanda ya dage wurin lalata kasar nan kuma daga bisani ya bace. Ya dace a ce ya na hutawa a gidan fursuna amma har yanzu sanatan shirme ya ke ta yi. Shugaban kasa ya na da kalamai a kan sa da kuma masu biye masa.
“Mun shirya damkarsa tare da gurfanar da duk wasu masu assasa tashin hankali da kalamansu ko ayyukansu. Babu shakka za mu cigaba da zama a Najeriya daya kuma mai cike da kwanciyar hankali.
“An shuka tsirran tashin hankali a zukatan jama'a ta hanyar kalamai. Miyagun magangansu sun kai wasu rayukan kaburburansu kuma sun sa an yi asarar kadarori masu yawa."

Bayan kwanaki 37, Buhari ya yi shiru kan nadin sabbin ministoci daga Kano da Taraba

A wani labari na daban, kwanaki 37 bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fatattaki ministoci biyu, Sabo Nanono da Saleh Mamman kan rashin kwazo, har yanzu shiru ake ji.

Kara karanta wannan

Ba ma son Biyafara, kawai muna so ayi mana adalci daidai da kowa ne - Gwamna Umahi

Tun bayan sallamar ministocin biyu da aka yi a ranar 1 ga watan Satumba, manyan 'yan siyasan jihohin Kano da Taraba suna ta hango kujerun, Daily Trust ta ruwaito.

Duk da shugaban kasan ya sauya wa wasu ministoci ma'aikatu inda ya maye gurbin Nanono da Mamman, 'yan siyasan jami'iyyar mai mulki daga jihohin suke ta jajen tsaikon.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel