Gwamnati ta mayar da yara 360,000 da basa zuwa makaranta zuwa ajujuwa a Katsina
- Hukumomin ilimi a jihar Katsina sun bayyana cewa, akalla yara 360,000 ne suka shiga marakanta a kasa da shekaru biyu
- A baya rahotanni sun bayyana yadda jihar ke fama da adadi mai yawa na yaran da ba sa zuwa makaranta
- A halin da ake ciki, akalla akwai yara sama da 775,000 da ke gararanba a gari ba tare da zuwa makaranta ba
Katsina - Jaridar The Cable ta ruwaito cewa, Gwamnatin Katsina ta ce sama da yara 360,000 ne a jihar suka yi rajista a makarantu tun daga shekarar 2019.
Abdulmalik Bello, daraktan wayar da kan jama’a, Hukumar Ilimi ta bai-daya ta jihar Katsina (SUBEB) ne ya bayyana hakan a ranar Laraba 6 ga watan Oktoba.
Ya bayyana haka ne a wani taro da ‘yan jarida kan shirin komawa makaranta da kuma yakin neman canji da aka kaddamar a jihar.
A cewar NAN, Bello ya ce rahoton da aka buga a shekarar 2018 ya nuna cewa akwai kusan yara miliyan 1.137 da ba sa zuwa makaranta a fadin kananan hukumomi 34 na jihar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cewarsa:
"Daga wannan lokacin, gwamnatin jihar tare da hadin gwiwar UNICEF sun sanya matakan da suka dace don magance matsalar."
“Daga shekarar 2019 zuwa yau, mun sami damar mayar da yara sama da 360,000 makaranta.
Ya kuma bayyana cewa, duba da kididdigar da ake dashi, har yanzu akwai yara sama da 775,000 da basa zuwa makaranta a jihar, inji rahoton jaridar This Day.
Hakazalika ya bayyana burin hukumarsu ta mayar da yara 200,000 makaranta kafin karshen 2021 tare da tallafin da suke samu daga UNICEF.
Da yake magana kan ci gaban, Lawal Buhari-Daura, shugaban SUBEB na Katsina wanda Isa Muhammad, sakataren hukumar ya wakilta, ya ce cutar ta Korona ta shafi yin rajistar makaranta a cikin jihar.
A kalamansa:
"Mun fito da wannan shirin saboda, bayan shagalta da annobar, iyaye da yawa sun ki mayar da yaransu makaranta."
“Yara sun dade ba tare da koyarwa da koyo ba sakamakon barkewar annobar. Don haka, gangamin neman komawa makaranta ya zama dole.
Ya kuma bayyana bukatar iyaye da dalibai su ma canza su kan yadda suka fahimci karatu a jihar.
A bangare guda, da yake magana kan hanyoyin da za a bi wajen cimma manufar ya bayyana daya daga ciki da cewa:
"Yada bayanai yana da mahimmanci don cimma wannan manufa, saboda haka kafafen watsa labarai na daya daga cikin manyan hanyoyin cimma burin mu daga yanzu zuwa 2030."
A cewar Binta Abdulmumin, mai kula da UNICEF a ma'aikatar ilimi ta jihar, Kafur da Kankara sune ke da mafi yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a jihar.
Binta ta ce UNICEF da gwamnatin jihar za su kaddamar da shirin yin rajista a kananan hukumomin biyu da abin ya fi shafa domin karfafa karin yara su koma karatu.
Mun kashe Bilyan 2 wajen ciyar da daliban firamare a jihar Adamawa kadai, Hajiya Sadiya Farouq
A nata bangaren, Gwamnatin tarayya ta ce ta kashe akalla bilyan biyu wajen ciyar da daliban makarantun jihar Adamawa kadai karkashin shirin ciyar da dalibai a fadin tarayya.
Ministar tallafi da walwala, Hajiya Sadiya Umar Faoruq, ta bayyana hakan ne a taron bada kayan girki 50,000 ga gwamnatin jihar Adamawa ranar Asabar a Yola, rahoton Tribune.
Sadiya Farouq, wacce ta samu wakilcin Dr. Umar Bindir, jagoran shirin walwala ta kasa, yace shirin ciyar da dalibai na cikin manyan shirye-shirye hudu na ma'aikatar.
Asali: Legit.ng