Jami'ar Kashere a Gombe ta yi waje da wasu dalibai bisa aikata barna a jarrabawa

Jami'ar Kashere a Gombe ta yi waje da wasu dalibai bisa aikata barna a jarrabawa

  • Jami'ar Kashere ta gwamnatin tarayya a jihar Gombe ta kori wasu dalibanta bisa wasu dalilai
  • Wannan na zuwa ne daga hukumomin jami'ar inda suka bayyana dalilin korar daliban nasu
  • Hakazalika, jami'ar ta sanar da cewa, nan kusa za a fara karatun samester na gaba na kalandar bana

Gombe - A ranar Talata ne Jami’ar Tarayya ta Kashere da ke Jihar Gombe ta sanar da fatattakar wasu dalibanta 23 daga makaranta sakamakon laifin ta'ammuli da jabun sakamako da kuma ta'annuti a jarrabawa.

Jami'an jami'ar sun kuma amince da dakatar da dalibi daya na wucin gadi, Daily Nigerian ta ruwaito.

Wannan batu na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban yada labarai da hulda da jama'a a jami'ar, Suleiman Malami ya fitar, ranar Talata 5 ga watan Oktoba a jihar Gombe.

Read also

Matashi ya maka IGP, DG na DSS da wasu manya a kotu kan cin zarafin 'yan Shi'a

Wata jami'a a Gombe ta yi waje da dalibai 23 saboda satar amsa a jarrabawa
Jami'ar tarayya da ke kashere a jihar Gombe | Hoto: campusinfo.com.ng
Source: UGC

Malami ya ce matakin ya biyo bayan shawarwarin da majalisar dattijai ta jami'ar ta yi yayin taronta na 68 na yau da kullum da ya gudana a makon jiya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Punch ta nakalto shi yana cewa:

“Majalisar Dattawan Jami'ar a taronta na 68 na yau da kullum da aka gudanar a ranar 23 ga Satumba, 2021 ta yi la’akari da amincewa da korar su da tsatstsaura mataki kan aikin su nan take.”

Mista Malami ya ce an gano daliban da aka koran suna son buga jabun sakamakon jarrabawa da barna a jarrabawa.

An kusa dawowa karatu a jami'ar

Sanarwar ta kuma nakalto Kabiru Garba-Aminu, magatakardar jami’ar yana cewa an kammala shirye-shiryen dawowar dalibai cikin kwanciyar hankali na kalandar ilimi ta semester ta biyu ta 2020/21.

Mista Garba-Aminu ya yi kira ga iyaye da su tabbatar da cewa 'ya'yan su sun dawo makaranta a kan lokaci saboda za a fara karatu nan take.

Read also

Tashar Africa Magic ta DSTV na shirin wasan kwaikwayo kan uwargidar Buhari

Ya sake nanata kudirin mahukuntan jami’ar na samar da yanayi mai kyau na koyo don tabbatar da ba a sami matsala a zangon ba.

Magatakardar ya kuma bukaci al'ummomin da ke zagaye da jami'ar da su ba da hadin kai da goyan bayan gudanarwa da kuma daliban.

Jerin mutane 6 da ke da hannu a yawaitar magudin jarrabawa a Arewacin Najeriya, Prof. Salisu Shehu

Farfesa Salisu Shehu, kwararre a fannin ilimin shari'a kuma shugaban jami'ar Al-Istiqama da ke Sumaila a jihar Kano ya bayyana tushen matsalar magudin jarrabawa a kamarantun Arewacin Najeriya.

Farfesa ya bayyana hake yayin wata hira da wakilinmu na Legit.ng Hausa a farkon makon nan, inda ya bude maganganu da yawa da suke da alaka da karantarwa da ma harkar tabarbarewar ilimi a yankin Arewa.

A cikin hirar, wakilinmu ya masa tambaya kan asalin musabbabin satar amsa a jarrabawar makarantu tare neman sanin a ina matsalar ta soma; shin bangaren malamai ne ko kuma hukumomi ko ma dai daliban.

Read also

Da dumi-dumi: Shugaba Buhari ya yi ganawar sirri da Goodluck Jonathan

Farfesa Salisu Shehu ya amsa tambayar da aka masa kan tushen matsalar satar amsa a makaranta, inda ya bayyana cewa, gwamnati, hukumomin ili, iyaye, shugabannin makarantu, dalibai da malamansu su suka lalalata harkar ilimi.

Gwamnatin Buhari za ta fara biyan daliban digiri da NCE kudin kashewa

A wani labarin, Gwamnatin Tarayya ta amince da biyan N75,000 a matsayin alawus-alawus na kowane semester ga daliban da ke karatun digiri a fannin Ilimi a jami'o'in gwamnati a Najeriya, Punch ta ruwaito.

Hakanan, daliban NCE za su karbi N50,000 a matsayin alawus na kowane semester a wani kokarin gwamnati don jawo hankalin samar da kwararrun malaman makaranta kamar yadda Shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya) ya yi alkawari shekaran da ya gabata.

Ministan Ilimi, Adamu Adamu, ya sanar da hakan a ranar Talata 5 ga watan Oktoba, a bikin ranar malamai ta duniya da aka gudanar a Eagle Square da ke babban birnin tarayya Abuja.

Read also

Da duminsa: Masu garkuwa da mutane sun sace dalibar BUK a Kano

Source: Legit.ng

Online view pixel