Tashar Africa Magic ta DSTV na shirin wasan kwaikwayo kan uwargidar Buhari

Tashar Africa Magic ta DSTV na shirin wasan kwaikwayo kan uwargidar Buhari

  • Kamfanin nishadantarwa da ke karkashin MultiChoice, Africa Magic, ya na duba yuwuwar yin wasan kwaikwayo kan Aisha Buhari
  • Kamar yadda shugaban kamfanin ta Najeriya, Busola Tejumola ta sanar, su na shirin yin fim kan uwargidan shugaban Buhari
  • Kamfanin ya yi wani taron baje-koli ne a jihar Kano na kwana biyu inda sama da furodusoshi dari biyu suka halarta

Kano - Africa Magic, gagarumin kamfanin nishadantarwa mallakin MultiChoice, su na duba yuwuwar yin wasan kwaikwayo kan Aisha Buhari, uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Daily Trust ta ruwaito cewa, Busola Tejumola, shugaban tashar ta Najeriya, ta bayyana hakan ne a ranar Talata yayin da ta ke jawabi a taron kwana biyu da Africa Magic ta shirya na baje koli a jihar Kano, wanda aka kammala jiya.

Africa Magic na shirin shirya wasan kwaikwayo kan Aisha Buhari
Africa Magic na shirin shirya wasan kwaikwayo kan Aisha Buhari. Hoto daga dailytrust.com
Source: UGC

A takardar da MultiChoice ta fitar, taron da ta shirya an samu ya hade da taron shekara- shekara na kungiyar watsa labarai na Najeriya, BON, ya samar da dama ga furodusoshi wurin mu'amala kai tsaye da Africa Magic domin samun damar tallatawa da siyar da hajojinsu.

Read also

EFCC ta gurfanar da tsohon shugaban jami’a kan badakalar N260m

Taron wanda ya samu halartar sama da furodusoshi dari biyu daga arewacin Najeriya, na son samar da hanyar samun riba da nasara ga dukkan masu ruwa da tsaki, Tejumola tace.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Kasuwar baje kolin Africa Magic hanya ce da aka kirkiro wanda muke fatan zai samarwa da kowanne furodusa damar mu'amala da masu siya. Zai samar mana da damar mu'amala da furodusoshi domin gane yanayi da ingancin abinda suka kawo..
“Babu shakka wannan aikin zai kai mu kusan dukkan sassan kasar nan. Lokaci ya yi da arewa za ta sanar da duniya labarin ta. Babu wani lokaci da ya fi dacewa da ya wuce yanzu," tace.

Fallasar handama: An matsa wa Buhari lamba kan ya bincike Bagudu, Obi da sauransu

A wani labari na daban, ana cigaba da matsanta wa shugaban kasa Muhammadu Buhari lamba kan ya binciki daya daga cikin makusantansa, gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu, tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi da dukkan 'yan Najeriya da bincike ya bayyana sun adana kazamar dukiya a duniya.

Read also

Buhari ya ce gwamnatinsa ta shirya za ta fara kera makamai saboda wasu dalilai

Takardun Pandora da aka saki a wannan makon ya fallasa sirrin kazamar dukiyar wasu shugabannin duniya, 'yan siyasa da biloniyoyi da suka hada da masu fadi a ji a Najeriya.

Baya da Bagudu da Obi, akwai tsohon babban alkalin Najeriya, 'yan majalisa masu ci yanzu da tsoffin 'yan majalisa, fasto da kuma wasu manya a kasar nan da aka gano da hannu cikin satar kudade tare da boye kadarori a kasashen ketare.

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel