Matashi ya maka IGP, DG na DSS da wasu manya a kotu kan cin zarafin 'yan Shi'a

Matashi ya maka IGP, DG na DSS da wasu manya a kotu kan cin zarafin 'yan Shi'a

  • Wani matashi ya shigar da kara kan cin zarafin 'yan Shi'a da aka yi a kwanakin baya
  • Ya bayyana wasu mutane shida da yake kara kan rashin adalci ga 'yan uwansa na kungiyar
  • Ya bayyana bukatunsa cikin takardar karar da majiyoyi suka ambata sun gani a kotu

An maka Darakta janar na hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da Sufeto janar na 'yan sandan Najeriya a kotu bisa zargin cin zarafi da kuntatawa mabiya akidar Shi'a karkashin jagorancin Malam Zakzaky.

Hakazalika, an kuma shigar har da rundunar Sojojin Najeriya, Sojojin Sama na Najeriya, Kwamandan Janar na NSCDC da Babban Lauyan Tarayya (AGF) a matsayin na uku zuwa na 6 wadanda ake tuhuma bi da bi.

Suleiman Sadi ne ya shigar da karar a ranar Litinin 4 ga watan Oktoba, a ruwayar jaridar Daily Sun.

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi Da Shugaban CAN Sun Buƙaci a Kama Musulmin Da Suka Kashe Fasto a Kano

Babbar magana: Matashin dan Shi'a ya maka IGP, DG na DSS da wasu manya a kotu
'Yan Shi'a mabiya Zakzaky | Hoto: Al Mizan
Asali: Twitter

A cikin sammacin da Bala Dakum ya gabatar, IGP da DG na DSS, a cikin sammacin da aka kawo a karkashin Doka ta3, Dokoki 6 da 7 na Dokokin kungiyoyin kasa, 2009 na kotu, da sauransu, sune wadanda ake tuhuma na daya da na biyu.

Mai gabatar da kara mai shekaru 25, wanda ya yi zargin cewa jerin gwanon da aka yi a ranar 27 ga Satumba da 28 ga Satumba an gudanar da shi cikin lumana, ya ce harin da jami’an tsaro suka kai musu take hakkinsu ne.

Ya bayyana cewa, dangane da rantsuwar goyon baya, jami'an tsaro sun gargade su cewa ba su da 'yancin gudanar da wannan shagali na addini koda kuwa za su yi shi cikin lumana.

Ya bayyana bukatar kotu ta ba 'yan Shi'a damar gudanar da ayyukansu na addini a duk fadin kasar ciki har da babban birnin tarayya Abuja, kamar yadda dokar kasa ta tanada.

Kara karanta wannan

Burodi ya zama nama: Tsadar burudo da 'Pure water' ya addabi babban birni Abuja

Hakazalika, ya nemi kotu ta alanta rashin adalcin da jami'an tsaro suka yi wa 'yan uwansa a baya-bayan nan na kamu, tsarewa da kisa ba tare da wani dalili ba.

Ya kuma nemi kotu da ta umarci jami'an tsaron da ake kara da su kau da kai kan duk wasu bukukuwan da 'yan Shi'a ke yi a fadin kasar kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.

Game da kame, ya bukaci kotu ta umarci jami'an tsaro su daina kamewa, tsare da kashe 'yan Shi'a yayin da suke zagaye ko wani shagalinsu.

Ya kuma nemi kotu ta umarci IGP da ya kare mambobin Shi'a da kungiyarsu a duk inda suke don gudanar da aikin addini cikin lumana a kasar.

Har yanzu ba a mika batun ga alkali ba a lokacin hada wannan rahoton.

Idan baku manta ba, kwanakin da suka gabata kadan ne kotu ta wanke Malam Zakzaky da matarsa daga laifukan da ake zarginsa da su, inda ya fara kokarin barin Najeriya saboda wasu dalilai.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Gwamnatin Buhari ta ware biliyoyin Nairori ga likitoci, ladan dage yajin aiki

Yadda Kotu ta wanke Sheikh Zakzaky da matarsa, ta umarci a sake su

A wani labarin, Rahotanni da muke samu sun bayyana cewa, a yau 28 ga watan Yuli, an yanke hukunci kan Zakzaky da matarsa, inda tuni aka wanke su daga zargi.

A cewar lauyan Zakzaky, Barista Sadau Garba, kotun ta wanke waɗanda ake zargin daga zargi takwas da gwamnatin Jihar Kaduna ta gabatar mata.

Rahoton ya ce tuni bayan yanke hukuncin aka zarce da Zakzaky zuwa gida nan take, kuma ba a tsaya sauraran 'yan jarida ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel