Da duminsa: Masu garkuwa da mutane sun sace dalibar BUK a Kano

Da duminsa: Masu garkuwa da mutane sun sace dalibar BUK a Kano

  • Masu garkuwa da mutane sun sace dalibar jami'ar Bayero da ke Kano
  • An gano cewa, ta na kan hanyarta ta zuwa Rijiyar Zaki daga Janbulo a Keke Napep
  • Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kano, SP Kiyawa, ya tabbatar da aukuwar lamarin inda yace suna bincike

Kano - Sakina Bello dalibar jami'ar Bayero ce da ke jihar Kano wacce ta ke aji uku na karatun ilimin tsirrai. Masu garkuwa da mutane sun sace dalibar yayin da ta ke hanya tsakanin Janbulo da yankin Rijiyar Zaki ta jihar Kano a tsakiyar birnin Dabo.

Majiyoyi daga 'yan uwanta sun tabbatar da aukuwar lamarin ga Daily Nigerian inda suka ce an sace ta wurin karfe 3 na yammacin ranar Talata yayin da ta ke cikin Keke Napep a hanyarta ta zuwa gida.

Kara karanta wannan

'Yan sandan Katsina sun damke dan Nijar mai shekaru 18 da ke kai wa 'yan binidiga man fetur

Da duminsa: Masu garkuwa da mutane sun sace dalibar BUK a Kano
Jami'ar Bayero ta Jihar Kano | Hoto: buk.edu.ng
Asali: UGC

Zuwa safiyar Laraba, wadanda suka sace ta sun kira inda suka bukaci kudin fansa har naira miliyan Dari.

Mai magana da yawun rundunar 'yan Sandan jihar Kano, Abdullahi Kiyawa, ya ce 'yan sanda sun samu rahoton batan Sakina wurin karfe 3 na yammacin Talata kuma a take suka fara bincike.

Kiyawa mai mukamin mataimakin sufirtandan 'yan sanda, ya ce ana kokarin ganin an gano inda ta ke.

A rahoton Punch, Mai magana da yawun jami'ar Bayero da ke Kano, Lamara Azare, ya ce jami'ar ba karatu ta ke ba tun daga watan Yuli kuma za ta koma ranar 1 ga watan Nuwamba.

A cewarsa:

"Ba karatu su ke ba. A halin yanzu bamu da dalibai a cikin makaranta kuma ba mu samu rahoton satar wata daliba ba."

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Sanata na goyon bayan IPOB, ya ce akwai kungiyoyin aware a kudu sun fi 30

Boko Haram sun gurgunta mulki a Neja, sun kayyade shekarun aurar da 'ya'ya mata

'Yan ta'addan Boko Haram sun addabi jama'a mazauna karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja da su dinga aurar da 'ya'yansu mata a shekaru 12.

Daily Trust ta ruwaito cewa, mazauna yankin da lamarin ya shafa sun ce 'yan ta'addan sun ba su umarnin cewa kada su kuskura su saurari wata hukuma.

Daya daga cikin mazauna yankin kuma daga cikin matasan Shiroro mai suna Bello Ibrahim, ya sanar da Daily Trust cewa:

"A wani lokaci, suna kauyen Kawure, kauyen tsohon sanata mai wakiltar Niger ta gabas, David Umaru.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng