An kuma, wani mutum ya jefi Shugaban Faransa, Emmanuel Macron da ɗanyen ƙwai

An kuma, wani mutum ya jefi Shugaban Faransa, Emmanuel Macron da ɗanyen ƙwai

  • Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron wanda wani ya wanke da mari kwanaki ya kara ganin wani tozarcin
  • Yayin da Macron ya kai ziyara wani gidan cin abinci a ranar Litinin sai ya ji saukar kwai a kafadar sa alamar jifar sa aka yi da shi
  • Sai dai an yi gaggwar fitar da wanda ya yi jifar daga wurin inda Macron ya ce idan yana bukatar magana da shi zai saurare shi anjima

Faransa - Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron ya ji saukar kwai a kafadarsa bayan ya kai ziyara wani gidan cin abinci a kasar ta Faransa.

Kamar yadda SaharaReporters ta ruwaito, bayan jifar sa da kwai da wani ya yi, ya sauka a kafadar sa sannan ya fadi kasa ba tare da ya fashe a jikin sa ba.

Kara karanta wannan

Daga 1 ga watan Oktoba matsalolin Najeriya za su kau, inji hasashen wani Fasto

An kuma, wani mutum ya jefi Shugaban Faransa, Emmanuel Macron da ɗanyen ƙwai
Shugaban Faransa, Emmanuel Macron. Hoto: Ireporteronline.com
Asali: Facebook

Ya kai ziyara wani wurin cin abinci da Otal ne dake kudu maso gabashin birnin Lyon a ranar Litinin kamar yadda AFP ta ruwaito.

An yi gaggawar fitar da wanda ya yi jifar daga dakin yayin da Macron ya ke cewa zai so tattaunawa da shi anjima.

Kamar yadda SaharaReporters ta ruwaito, Macron ya ce:

“Idan ya na da wani abu da zai fada min, ya zo. Zan neme shi daga baya.”

Hayaniya ta yawaita bayan an yi wa shugaban kasan maraba da zuwa sai ya bayyana cewa wurin cin abincin ba za su sa haraji ga wadanda zasu yi amfani da katin banki wurin siyan abinci ba.

Ba Macron aka fara jifa da kwai ba a kasar

Masu zanga-zanga sun dade su na jefa wa ‘yan siyasar kasar Faransa kwai don haka ba Macron bane farau.

Kara karanta wannan

Ban taba son yarana su yi kama da ni ba domin ba ni da kyau: Jarumin fim ya magantu

A shekarar 2017 lokacin yana takarar shugabancin kasar, an jefe shi da kwai a kan sa bayan ya kai ziyara wani taron manoma a Paris.

A watan Yunin da ya gabata wani ya wanka masa mari yayin da yake tsaka da gaisawa da masoyan sa a kudancin birnin Valence.

Matashin da ya wanka masa mari mai shekaru 28 ya sha daurin watanni 4 a gidan gyaran hali bayan gabatar da shi a kotu da aka yi.

Anyi ta tunanin za a tsananta ma sa tsaro a watanni masu zuwa musamman idan zai bayyana a cikin jama’a idan zai yi yawon kafen don a zabe shi a karo na biyu.

Sai dai har yanzu bai bayyana ra’ayin sa na kara tsayawa takara ba don sake kwashe wasu shekaru 5 a kujerar sa duk da watan Afirilu mai zuwa ne za a sake zabe.

Wani Mutum Ya Sharara Wa Shugaban Faransa Emmanuel Macron Mari

Kara karanta wannan

El-Rufai: Arewa maso yamma ta rikice, kiyasin mu ya na kai da kai da Afghanistan

Tun a bayan, kun ji cewa wani mutum ya mari Shugaba Emmanuel Macron na kasar Faransa a ranar Talata yayin da ya tafi ganawa da mutanen gari a yankin kudancin kasar kamar yadda wani faifan bidiyo ya nuna, France 24 ta ruwaito.

Masu tsaron Macron sunyi gaggawa sun zakulo mutumin daga cikin dandazon mutane suka matsar da shi gefe. An kama wasu mutane biyu da hannu kan lamarin kamar yadda RMC radio ta ruwaito.

Reuters ta ruwaito cewa Farai Ministan Faransa Jean Castex ya ce lamarin karan tsaye ne ga demokradiyya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel