Sojin Najeriya sun cafke kasurgumin shugaban 'yan bindiga mai suna Goma Sama'ila
- Sojojin Najeriya sun samu nasarar cafke wani bata-gari shugaban 'yan bindiga da ake nema ruwa a jallo
- A rahoton da muka samu, an bayyana cewa, yana daya daga cikin 'yan ta'addan da suka addabi yankin Arewa masi yamma
- Kada ku manta, jihohi a yankin Arewa masi yamma na ci gaba da fuskantar matsololi tsaro
Rundunar Sojin Najeriya ta samu nasarar cafke shugaban ‘yan bindiga da barayin shanu, Alhaji Goma Sama’ila.
Legit.ng Hausa ta tattaro daga jaridar SaharaReporters cewa, an damke Samaila ne a jihar Kaduna da yammacin Juma’a 24 ga watan Satumba.
Rahotannin shaidun gani da ido sun nuna cewa Sama’ila ne ke da alhakin shirya satar shanu da dama a jihohin Zamfara, Kaduna, Katsina da sauran jihohin Arewa maso Yammacin Najeriya.
An ce yana cikin wasu ayyunkan barna na garkuwa da mutane da dama a fadin jihohin.
Jihar Kaduna tana ci gaba da shan fama da barnar masu garkuwa da mutane, kisan gilla da satar shanu daga 'yan bindiga.
Wata majiya ta ce:
“Sojojin Najeriya sun cafke Goma Sama’ila, daya daga cikin “ wadanda ake nema” kuma kasurguman shugabannin 'yan bindiga da ke addabar Zamfara, Kaduna, Katsina da sauran jihohin arewa maso yammacin Najeriya.
Wannan ci gaba na zuwa ne yayin da sojoji ke aikin kakkabe 'yan ta'adda a yankin.
A baya mun kawo muku rahoton cewa, an kashe hanyoyin sadarwa a jihar Zamfara don shawo kan matsalolin tsaro da suka addabi jihar.
Jihar Katsina, duk da kasancewar mahaifar shugaban kasa Muhammadu Buhari, ta sha fuskantar hare-haren ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane wanda ya yi sanadiyyar salwantar rayuka da dama.
Fiye da mutane 700 ne 'yan bindiga suka kashe a kananan hukumomin Jibia, Kankara, Dutsinma, Musawa, Danmusa da Safana na jihar a cikin watanni biyar da suka gabata.
Gwamnatin jihar Sakkwato ta kuma katse hanyoyin sadarwa a kananan hukumomi 14 cikin 23 na jihar a wani bangare na kokarin kakkabe 'yan ta'adda a dazukan jihar.
'Yan bindiga sun sace dalilan jami'a kwanaki kadan bayan sace malamansu
Wasu 'yan bindiga sun sace dalibai 10 na Jami'ar Jihar Abia, Uturu (ABSU) a hanyar Ihube zuwa ABSU, Daily Sun ta ruwaito.
Sace daliban na zuwa ne makonni bayan da wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da malaman jami’ar uku a kan hanyar Uturu/Isuikwuato.
Lamarin wanda rahotanni suka ce ya faru tsakanin karfe 5 na yamma zuwa 6 na yamma a ranar Asabar, ya jefa al’ummar jami’ar cikin rudani.
An ba da rahoton cewa motar bas ta jihar Abia da ke jigilar fasinjoji zuwa makarantar, SUV da mota kirar Hilux mallakar wani kamfani an same su babu kowa a ciki a wurin da lamarin ya faru, abin da ke nuni da cewa ba daliban kadai aka sace ba.
Rahoto: Halin da ake ciki na harin 'yan bindiga duk da katse hanyoyin sadarwa a Zamfara
A wani labarin, alamu sun bayyana cewa har yanzu ana ci gaba da samun kashe-kashe da garkuwa da mutane a jihar Zamfara duk da katse hanyoyin sadarwa a jihar.
Yayin da katsewar da kokarin sojoji ya rage barnar 'yan bindiga tare da kashe su, wasu mazauna jihar sun shaida wa BBC Hausa cewa an ci gaba da kai hare-hare da sace-sacen a jihar.
Don haka, duk da rokon da suke yi wa gwamnatin jihar na tsagaita wuta, kamar yadda Gwamna Bello Matawalle ya bayyana a ranar 10 ga Satumba, 'yan bindigan sun ci gaba da kai hari kan mazauna jihar.
Asali: Legit.ng