Badakalar $65m: Auren Ya'u Kumo da diyar Buhari ya mutu, yanzu ba suruki bane, Garba Shehu

Badakalar $65m: Auren Ya'u Kumo da diyar Buhari ya mutu, yanzu ba suruki bane, Garba Shehu

- Fadar shugaban kasa ta nesanta Buhari da mutumin da ake nema ruwa a jallo

- Hukumar ICPC ta yi shelan neman Alhaji Ya'u Kumo kan badakalar wasu kudade

- Ya'u Kumo ya kasance tsohon Diraktan bankin FMBN

Fadar shugaban kasa ta alanta cewa mutumin da hukumar yaki da rashawa ta ICPC ke yiwa zargin badakalar $65m ba surukin shugaba Buhari bane kamar yadda ake yadawa.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Juma'a a Abuja.

ICPC ta alanta neman Gimba Ya'u Kumo ruwa a jallo kan badakalar dala milyan 65.

Ya'u Kumo ya kasance tsohon Dirkatan Bankin gine-gine, kuma ya auri diyar Buhari a Oktoban 2016 a Daura, jihar Katsina.

Amma fadar shugaban kasa na bayyana cewa auransu ya mutu.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin sabon shugaban Chadi, Mahamat Deby

Badakalar $65m: Auren Ya'u Kumo da diyar Buhari ya mutu, yanzu ba suruki bane, Garba Shehu
Badakalar $65m: Auren Ya'u Kumo da diyar Buhari ya mutu, yanzu ba suruki bane, Garba Shehu Hoto: Channels TV
Asali: Twitter

DUBA NAN: An damke tsagerun yan bindiga 5 a Zamfara da muggan makamai

Wani sashen jawabin yace: "Wani labari da ake yadawa cewa ICPC na neman surukin Buhari ruwa a jallo kan badakalar kudi dala milyan 65."

"Gaskiyar magana itace, mutumin da ake nema ruwa a jallo ba surukin shugaba Buhari bane."

"Duk da cewa an taba alakar aure tsakaninsa da iyalin Buhari, auren ya mutu wasu yan shekaru da suka wuce."

A bangare guda, Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Alhamis ya bayyana cewa gwamnatinsa na namijin kokarin wajen magance matsalar tsaron da ta addabi Najeriya.

A bayaninsa, Buhari yace yana fatan yan Najeriya zasu gane irin kokarin da sukeyi.

Buhari ya bayyana hakan ne a hira da manema labarai bayan halartan Sallar Idi a fadar shugaban kasa, Aso Villa, Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel