Daga Obasanjo zuwa Buhari: Jerin basussuka da aka karbo a karkashin Shugabannin Najeriya 4

Daga Obasanjo zuwa Buhari: Jerin basussuka da aka karbo a karkashin Shugabannin Najeriya 4

Kwanan nan, Shugaba Muhammadu Buhari ya haifar da zazzafan martani daga 'yan Najeriya lokacin da ya gabatar da wata sabuwar bukata don amincewa da ciyo sabon bashi a gaban Majalisar Dattawa.

Shugaban na Najeriya ya nemi amincewar Majalisar Dokoki ta kasa don karbo bashin $4,054,476,863.00, €710 miliyan da tallafin dala miliyan 125.

Daga Obasanjo zuwa Buhari: Jerin basussuka da aka karbo a karkashin Shugabannin Najeriya 4
Daga Obasanjo zuwa Buhari: Jerin basussuka da aka karbo a karkashin Shugabannin Najeriya 4 Hoto: Femi Adesina, Goodluck Jonathan, BBC Hausa
Asali: Facebook

Da yawa daga cikin ‘yan Najeriya na adawa da yadda gwamnatin mai ci ke ci gaba da karbo basussuka yayin da take kokarin samar da karin ababen more rayuwa a yayin da ake samun raguwar kudaden shiga.

Bashin da ake bin Najeriya ya na karuwa. Ya zuwa watan Maris na 2021, yawan bashin da ake bin Najeriya ya kai naira tiriliyan 33.1 (dala biliyan 87.24); tarin basussuka daga gwamnatocin da suka biyo juna.

Kara karanta wannan

Abubuwa 7 da Shugaba Buhari ya fada a jawabin da yayi a majalisar dinkin duniya

Kwanaki jaridar The Cable ta ruwaito cewa duk da samun nasarar yafe bashi a lokacin gwamnatin Olusegun Obasanjo, gwamnatocin da suka biyo baya sun ci gaba da ciyo bashi.

Jaridar ta bayyana cewa bashin da ɓangaren gwamnatin tarayya ta ciyo ya haura kashi 658% zuwa naira tiriliyan 26.9 a cikin shekaru 21 da suka gabata.

Da yake ambaton bayanai daga Ofishin Kula da Bashi (DMO), rahoton ya bayyana cewa bashin gwamnatin tarayya (bashin cikin gida da na waje) ya haura daga naira tiriliyan 3.55 a 1999 zuwa naira tiriliyan 26.91 a karshen Maris 2021 (sabon adadi na kasar).

Tun 1999 lokacin da Najeriya ta dawo kan turbar dimokuradiyya, Najeriya ta samu shugabanni hudu, Olusegun Obasanjo, Umaru Yar'Adua, Goodluck Jonathan da Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

Bikin tunawa da ranar 'yancin kai: FG ta yi gargaɗi mai ƙarfi ga 'yan Najeriya gabanin 1 ga Oktoba

Wannan rahoton ya duba basussukan da aka karba a karkashin gwamnatocin guda hudu.

1. Tsohon Shugaban kasa Obasanjo

Bashin waje: Ya ragu daga dala biliyan 28.04 a 1999 zuwa dala biliyan 2.11 a 2007

Bashin cikin gida: Ya karu daga naira biliyan 798 zuwa naira tiriliyan 2.7

Bashin FG: Ya ragu daga naira tiriliyan 3.55 a 1999 zuwa naira tiriliyan 2.42 a shekarar 2007

Matakin bashin FG na gida da waje: raguwar kashi 31.8%

Darajar kudi: N98.02/N116.8 kan $ 1

Abun lura: Babban koma baya a cikin bashin kasashen waje ya kasance saboda raguwar da aka samu sakamakon biyan basussukan da ake bin Ƙungiyoyin Masu Ba da Lamuni na London a farkon kwata na 2007.

2. Yar'Adua/Jonathan (2007 to 2011)

Bashin kasashen waje - Ya karu daga dala biliyan 2.11 a 2007 zuwa dala biliyan 3.5 a 2011

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: AMCON ta ƙwace katafaren gidajen tsohon gwamnan Kwara Abdulfatah Ahmed

Bashin cikin gida: Ya karu daga Naira tiriliyan 2.7 a 2007 zuwa Naira tiriliyan 5.62 a 2011

Darajar kudi: Ya karu daga N116.8 / $ 1 zuwa N156.7 / $ 1.

Karuwar kashi: 155%

Abun lura: Daga cikin adadin bashin, Jonathan ya kammala wa’adin mulkin daga Mayu 2010 zuwa Mayu 2011 bayan rasuwar Yar’Adua. A cikin wannan lokacin, an bayar da rahoton cewa bashin ya tashi daga naira tiriliyan 4.94 zuwa tiriliyan 6.17 (karuwar kashi 24.9 cikin shekara daya).

3. Tsohon Shugaban kasa Jonathan

An fara mulkin (2011):

Bashin waje: dala biliyan 3.5

Bashin cikin gida: tiriliyan N5.62

An tattara bashin Naira tiriliyan 6.17.

2014

Bashin kasashen waje - dala biliyan 6.45

Bashin cikin gida - Naira tiriliyan 7.9 (Canjin kudin kuma ya tsaya akan N197/$ 1)

Jimlar bashin gwamnati (2011 zuwa 2015): Ya karu daga naira tiriliyan 6.17 a 2011 zuwa naira tiriliyan 9.8 a 2015 (Karin N3.63 tiriliyan)

Kara karanta wannan

Obasanjo ga Buhari: Ta'addanci ne a yi ta karbo bashi ana barin na baya da biya

Karuwar kashi: 58.8%

4. Shugaba Buhari

2015:

Bashin waje: Dala biliyan 7.35

Bashin cikin gida: Naira tiriliyan 8.84

Kimar FX: 197

2020

Bashin waje: $ 28.57 biliyan

Bashin cikin gida: Naira tiriliyan 16.02

Bashin cikin gida: Ya karu da naira tiriliyan 7.63 (Yuni 2015 zuwa Disamba 2020)

Bashin waje: Ya karu da dala biliyan 21.27 (daga watan Disambar 2020)

FX: N381 (2020)

Ƙaruwar kashi: 173.2% daga 2015

A cewar rahoton The Cable, Shugaba Buhari shine babban mai ciyo bashi a kasar, inda ya kara yawan bashin gwamnati (bangaren FG) da sama da kashi 173%.

Gwamnatin Yar’Adua / Jonathan ce ta zo ta biyu tare da karuwar kashi 155% na bashi.

Gurbi na uku yana karkashin gwamnatin Jonathan wanda ya sami karuwar kashi 58.8%.

A cikin gwamnatoci hudu da suka gabata, gwamnatin Obasanjo ce kadai ta rage bashin da ake bin gwamnati.

Kara karanta wannan

Gagarumin matsala ya fara yayin da majalisa ta yi barazanar kama wasu manyan nade-naden Buhari

Babu yadda mukayi iya, ba zamu iya hana Buhari karban bashi ba: Ahmad Lawan

A gefe guda, Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya bayyana dailin da yasa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ke cigaba da ciyo basussuka.

A jawabin da yayi bayan sauraron rahoton shugaban kwamitin MTEF, Olamilekan Adeola, Sanata Lawan ya yi watsi da maganar Sanatoci cewa gwamnatin Buhari na cin bashi da yawa.

Shugaban majalisar ya bayyana cewa babu yadda aka iya da cin bashin da Buhari ke yi, rahoton Tribune.

Asali: Legit.ng

Online view pixel