Abubuwa 7 da Shugaba Buhari ya fada a jawabin da yayi a majalisar dinkin duniya
A ranar Juma'a, 24 ga Satumba, Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar da jawabi gaban shugabannin duniya a taron gangamin majalisar dinkin duniya UNGA76 dake gudana yanzu haka a birnin New York dake Amurka.
Buhari ya yi magana kan yada za'a farfado daga annobar COVID-19, sauyin yanayi, kare hakkin mutane da sauran su.
1. COVID-19
Shugaba Buhari ya gidewa duniya bisa matakin da suka dauka wajen dakile cutar COVID-19.
Ya bayyanawa duniya cewa gwamnatinsa na iyakan kokari wajen dakile cutar kan yan Najeriya.
2. Safara Makamai
Shugaba Buhari ya bayyana alhininsa kan yadda ake kasuwancin makamai ba bisa doka da tsari ba.
A cewarsa, yada ake safara miyagun makamai na da illa ga rayuwa da tattalin arzikin kasashen Afrika.
3. Ta'addanci
Shugaban Najeriyan ya bayyana cewa gwamnatinsa zata cigaba da hada dai da hukumomin yaki da ta'addanci na majalisar dinkin duniya saboda yadda lamari ke tsamari a fadin duniya.
Ya bayyana cewa an nakasa kungiyar Boko Haram a Najeriya amma har yanzu suna kai hare-hare.
4. Sauyin Yanayi
Buhari ya bayyana illar sauyin yanayi kan Najeriya, inda yace an fari ganin illar hakan a bushewar tekuna, gudun hijra da kuma rashin abinci.
5. Dukiyoyin sata
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasan yace kokarin da sukayi na kwato kudaden sata da wasu suka boye a kasashen waje ya taimaka wajen samun kudaden amfani lokacin yaki da annobar Korona.
6. Rashawa
Ya kara da cewa har ila yau Rashawa na da mumunan illa gazaman lafiya da tattalin arziki, musamman a kasashe masu tasowa irin Najeriya.
7. Kare hakkin dan Adam
Shugaban Najeriyan ya bayyana cewa kasarsa ba zata yi kasa a gwiwa wajen cigaba da kare hakkin dan Adam ba.
Shugaba Buhari ya tafi New York don halartar taron UNGA a ranar Lahadi
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bar Abuja a ranar Lahadi, 19 ga watan Satumba zuwa birnin New York a Amurka.
Legit.ng ta rahoto cewa shugaban kasar zai halarci taro na 76 na babban zauren Majalisar Dinkin Duniya (UNGA76). An bude taron ne a ranar Talata, 14 ga watan Satumba
Asali: Legit.ng