Obasanjo ga Buhari: Ta'addanci ne a yi ta karbo bashi ana barin na baya da biya

Obasanjo ga Buhari: Ta'addanci ne a yi ta karbo bashi ana barin na baya da biya

  • Tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo ya koka kan yawaitar bashin da Najeriya ke ci
  • Ya bayyana cewa, tara bashin ga masu zuwa nan gaba ta'addanci ne da bai kamata ya ci gaba da faruwa ba
  • Ya bayyana haka ne yayin da yake martani kan bukatar da shugaba Buhari ya mika na sake cin wani bashi

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya yi kaca-kaca da shirin gwamnatin tarayya na ciyo sabon bashi na kasashen waje, kuma ci gaba da tara bashin ta'addanci ne, Daily Trust ta ruwaito.

Ya ce gwamnatin Buhari na tara basussuka ne ga masu zuwa a bayanta, yana mai bayyana hakan a matsayin "ta'addanci."

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata ya gabatar da bukatar neman amincewa don karbo sabbin basussuka na kasashen waje na $4.054bn da €710m ga majalisar kasa.

Kara karanta wannan

Fitaccen Sanatan APC ya nuna damuwa kan yadda majalisa ke saurin amincewa Buhari ya ciyo bashi

Obasanjo ga Buhari: Ta'addanci ne a yi ta karbo bashi a bar na baya da biya
Tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo | Hoto: thecable.ng
Asali: Facebook

Bukatar tana cikin wasikar da shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan ya karanta a zaman zauren majalisar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cikin wasikar, Buhari ya bayyana cewa saboda “bukatu masu tasowa,” akwai bukatar tara karin kudade don wasu “manyan ayyuka”.

Martanin Obasanjo kan yawaita cin bashi

Da yake magana a gidan talabijin na Channels yayin wani taron da aka yi a Afirka ta Kudu, Obasanjo ya ce idan aka bar bashin da ake da shi ba tare da an duba ko an biya shi ba, yana iya zama matsala ga gwamnatocin gaba.

Yayin da yake bayyana cewa cin bashi ba shine matsala ba, tsohon shugaban na Najeriya ya ce abin da zai iya zama matsala shi ne abin da mutum ya ci bashin dominsa da kuma tsara shirin biya.

Legit.ng Hausa ta tattaro daga TheCable inda Obasanjo ke cewa:

Kara karanta wannan

Janar Faruk Yahaya: Za mu ji da 'yan bindiga da yaren da suke fahimta

“Idan kana son gina gidan kasuwanci kuma ka je ka karbi kudi, kana da 50% na kudin ka, sannan ka karbi bashin 50% kuma a cikin shekaru biyar, ka biya 50% din da ka karbo. Wannan hikima ta yi.
"Amma idan za ka je ka nemi bashin kudi don ka iya ciyar da kanka da iyalanka, wannan abin wauta ne.
Don haka, idan muna cin bashi don ci gaba da kashe kudi, wannan babban wauta ne. Idan muna cin bashi ne don ci gaban da bashin zai iya biyan kansa, wannan abu ne mai kyau. Sannan biyan bashin, tsawon wane lokacin zai dauka kafin a biya?
"Amma muna cin bashi da tara bashi ga masu zuwa a baya, ta'addanci ne, a saukakakken harshe. Don me muke cin bashi? ”

Ya tuna cewa a lokacin mulkin sa a 1999, kasar na kashe $3.5bn don biyan basussukan da ke ci gaba da karuwa.

Kara karanta wannan

Ministan Buhari: Mu ilmantar da 'yan Najeriya ko kuma su addabi kasa da manyan kasa

Ya kara da cewa:

"Lokacin da na shiga gwamnati a matsayin zababben shugaban kasa, muna kashe $3.5bn don biyan bashi. Ko da hakan, yawan bashin da ake binmu bai ragu ba,"

Dalilin da yasa mambobin APC ke jin haushin shigowar Kayode jam'iyyarsu, DG PGF

A wani labarin, Salihu Lukman, darakta janar na kungiyar gwamnonin ci gaba (PGF), ya bayyana dalilin da ya sa wasu mambobin jam’iyyar APC ke adawa da sauya shekar Femi Fani-Kayode zuwa cikinta.

A ranar Alhamis, tsohon ministan sufurin jiragen sama ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC sannan aka gabatar da shi ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa, Abuja.

Sauya shekar tsohon ministan ya jawo cece-kuce mai zafi daga dubban 'yan Najeriya da dama, ciki har da mambobin APC, TheCable ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel