Yanzu-Yanzu: AMCON ta ƙwace katafaren gidajen tsohon gwamnan Kwara Abdulfatah Ahmed

Yanzu-Yanzu: AMCON ta ƙwace katafaren gidajen tsohon gwamnan Kwara Abdulfatah Ahmed

  • Kotu ta bawa hukumar AMCON izinin kwace gidaje da filayen tsohon gwamnan Kwara Abdulfata Abdulrazaq
  • Hukumar ta AMCON ta yi karar Abdulfatah ne a kotu bisa bashin Naira Biliyan 5 da ta ke binsa kuma ta ga ba shi da niyyar biya
  • Mai magana da yawun AMCON, ya tabbatar da hakan yana mai cewa sunyi kokarin warware matsalar ta hanyar diflomasiyya amma bai yiwu ba

Hukumar Kula da Kadarorin Najeriya, AMCON, ta kwace katafaren gidan tsohon gwamnan jihar Kwara, Abdulfatah Ahmed da kudinta ta dara naira biliyan biyar, (N5bn) The Cable ta ruwaito.

A.M. Liman, alkali a kotun tarayya na Legas ne ya bawa AMCON umurnin hakan a ranar Laraba 22 ga watan Satumba.

Yanzu-Yanzu: AMCON ta ƙwace katafaren gidan tsohon gwamnan Kwara Abdulfatah Ahmed
AMCON ta ƙwace katafaren gidan tsohon gwamnan Kwara Abdulfatah Ahmed. Hoto: The Cable
Asali: Facebook

Alkalin ya kuma bada umurnin a rufe asusun ajiyar banki na tsohon gwamnan da kamfanoninsa biyu; Trans Properties and Investment Limited and Trans It Consulting Limited.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Sarkin Gaya a jihar Kano ya rigamu gidan gaskiya

Gidajen suna rukunin gidajen gwamnati na a Abdulrazaq road, GRA, Ilorin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jude, Nwazor, mai magana da yawun AMCON ya tabbatar wa Daily Trust afkuwar lamarin.

Ahmed, wanda ya gaji tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ya mulki jihar Kwara daga 2011 zuwa 2019.

Dalilin da yasa AMCON ta yi karar tsohon gwamnan a kotu

Nwauzor ya ce duk da cewa Abdulfatah ya rike babban matsayi a Nigeria, ya gaza biyan bashin na kansa da ya karba.

Wani sashi na sanarwar ta ce:

"Bisa umurnin kotu a yau, AMCON ta hannu lauyoyin ta a Robert Ohuoba & Co na Cif Robert, daya daga cikin masu hulda da kamfanin kula da kadarori na AMCON sun kwace katafaren gidan tsohon gwamnan jihar Kwara da ke Abdulfatah Street, GRA, Ilorin, Jihar Kwara."

Ya kuma ce AMCON din ta kwace asusun ajiyar bankin tsohon gwamnan a wasu bankuna na zamani da kamfaninsa na Trans Properties and Investment Limited and Trans It Consulting Limited.

Kara karanta wannan

Attahiru Jega da wasu manyan Najeriya sun kirkiri sabuwar jam'iyyar ceto Najeriya

Sanarwar ya cigaba da cewa AMCON ta fara binciko kadarorin tsohon gwamnan ne inda ta gano yana da wasu gidajen a Kwara, Legas da babban birnin tarayya Abuja kuma tana shirin kwace su.

Hakan ya yi dai-dai da tanadin sashi na 49(1) na dokar AMCON na 2019 (Da aka yi wa kwaskwarima) wacce ta ce idan har kamfani tana da hujjar ganin wanda ake bi bashi ba shi da niyyar biya, tana iya neman izini daga kotu domin bin hakkinta ta hanyar kwace kadarorinsa.

Sauran kadarorin Abdulrazaq da kotu ta bawa AMCON izinin kwace wa

Sauran kadarorin tsohon gwamnan da kotu ta bawa AMCON izinin kwacewa sun hada da gida a No 13, Alhaji Masha Road, Surulere; No. 9 Wharf, Apapa, Lagos; Plot 3632, Cadastral Zone E27 of Apo, Abuja; Plot 4115, Cadastral Zone F14 of Bazango, Abuja; Plot 8502, Cadastral Zone E31 of Carraway Dallas, Abuja; Plot 494, Cadastral Zone E31 of Carraway Dallas, Abuja; Plot 719, Cadastral Zone E23 of Kyami, Abuja.

Kara karanta wannan

Hotunan shugaban EFCC yayin da ya gurfana a gaban kotu domin bada shaida

Kotun ta kuma kara da cewa AMCON ta kwace duk wani fili ko gida mallakar Abdulfatah a Nigeria.

'Yan sanda sun damke ma'aikacin banki da ya kwashewa kwastoma N10m daga asusunsa

A wani labarin daban, Hukumar ‘yan sandan jihar Oyo sun kama wani Adeyemi Tosin, mai shekaru 36, wanda ma’aikacin banki ne bisa zarginsa da kwasar naira miliyan 10 daga asusun wani abokin huldar bankin, Oladele Adida Quadri.

Kakakin hukumar, DSP Adewale Osifeso, ya bayyana hakan a wata takarda a ranar Talata, 17 ga watan Augusta, inda yace Tosin ya saci kudin Quadri, mai shekaru 78 ne da sunan zai taimake shi a reshen bankin na Ibadan bisa matsalar da ya samu wurin cirar kudi a ranar 12 zuwa ranar 13 ga watan Augusta.

Binciken ‘yan sandan ya haifi da mai ido sakamakon umarnin kwamishinan ‘yansandan jihar, Ngozi Onadeko, wacce tasa a yi bincike na musamman.

Kara karanta wannan

Akwai yuwuwar dan siyasan Najeriya da U.S., UK ke tuhuma ya zama gwamna

Asali: Legit.ng

Online view pixel