Bikin tunawa da ranar 'yancin kai: FG ta yi gargaɗi mai ƙarfi ga 'yan Najeriya gabanin 1 ga Oktoba

Bikin tunawa da ranar 'yancin kai: FG ta yi gargaɗi mai ƙarfi ga 'yan Najeriya gabanin 1 ga Oktoba

  • Yayin da ake shirye-shiryen bikin cika shekaru 61 da samun 'yancin kai na kasar, gwamnatin tarayya ta ja hankalin al'umman babbar birnin tarayya game da lamarin tsaro
  • Wannan gargadin na kunshe ne cikin wata sanarwa da Ministan Yada Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed ya fitar a Abuja
  • An bukaci mazauna yankin da su kai rahoton duk wani mutum da motsi da basu yarda da shi ba zuwa ga hukumomin tsaro da suka dace

Abuja - Gwamnatin Tarayya ta fadakar da jama'a da su kara tsaurara matakan tsaro don shirye -shiryen bikin cika shekaru 61 da samun 'yancin kai na kasar.

Ministan Yada Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja, a ranar Juma’a, 24 ga Satumba, ta hannun mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Segun Adeyemi.

Kara karanta wannan

Daga 1 ga watan Oktoba matsalolin Najeriya za su kau, inji hasashen wani Fasto

Bikin tunawa da ranar 'yancin kai: FG ta yi gargaɗi mai ƙarfi ga 'yan Najeriya gabanin 1 ga Oktoba
Bikin tunawa da ranar 'yancin kai: FG ta yi gargaɗi mai ƙarfi ga 'yan Najeriya gabanin 1 ga Oktoba Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Mohammed, ya yi kira ga mazauna Babban Birnin Tarayya da kewayenta da kada su firgita kuma su ci gaba da ayyukansu na halal.

Ya ce:

“An umarci mazauna yankin da su kai rahoton mutane da motsin da basu aminta da shi ba zuwa ga hukumomin tsaro ta wadannan lambobi: 09-6305396, 08031230631, 08032003557 da 122.''

Daga 1 ga watan Oktoba matsalolin Najeriya za su kau, inji hasashen wani Fasto

A wani labarin, babban Limami na Deeper Christian Life Ministry (DCLM), Fasto William Kumuyi, ya ce rashin tsaro, zalunci da azabtarwa duk za su kau yayin da Najeriya ke murnar zagayowar ranar samun 'yancin kai na wannan shekara a ranar 1 ga Oktoba.

Kumuyi ya fadi haka ne a lokacin da ya isa Abuja don yin taron gumurzu na kwanaki 5 mai taken, “Divine Solution Global”, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

NDLEA Ta Kama Dillalin Miyagun Kwayoyi Da Hodar Iblis Na Biliyan 2.3 A Abuja

Ya kuma yi kira da a tattauna ko a yi zaman fahimtar juna tsakanin bangarori domin samun mafita ta dindindin a danbarwar da ke likitoci mazauna Najeriya da Gwamnatin Tarayya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel