Babu yadda mukayi iya, ba zamu iya hana Buhari karban bashi ba: Ahmad Lawan

Babu yadda mukayi iya, ba zamu iya hana Buhari karban bashi ba: Ahmad Lawan

  • Shugaban majalisa yace dole ce ta sa Najeriya na cigaba da karban basussuka
  • Sanatan ya daura laifi kan shugabannin baya da suka ki yin abinda ya kamata
  • Hakazalika Lawan yayi kira ga Sanatoci da shugabannin kwamitoci su tashi tsaye

Abuja - A ranar Laraba, Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya bayyana dailin da yasa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ke cigaba da ciyo basussuka.

A jawabin da yayi bayan sauraron rahoton shugaban kwamitin MTEF, Olamilekan Adeola, Sanata Lawan ya yi watsi da maganar Sanatoci cewa gwamnatin Buhari na cin bashi da yawa.

Shugaban majalisar ya bayyana cewa babu yadda aka iya da cin bashin da Buhari ke yi, rahoton Tribune.

Ya daura laifin kan gwamnatocin da suka shude inda ta tuhumesu da rashin basira da tunani.

Kara karanta wannan

Obasanjo ga Buhari: Ta'addanci ne a yi ta karbo bashi ana barin na baya da biya

Yace:

"Kwamitin tayi aiki mai kyau. Idan ba'ayi abinda ya kamata lokacin da ya kamata ba, irin wannan halin ake shiga. Mun yi almubazzaranci da dukiyoyinmu lokacin da muke da su da yawa."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Yanzu abubuwan sun matse mana. Na san akwai bukatar mu rage karban bashi amma kwamitin kudi na kokarin ganin cewa ma'aikatun gwamnati sun kara kudin shigar da gwamnati ke samu."

Babu yadda mukayi iya, ba zamu iya hana Buhari karban bashi ba: Ahmad Lawan
Babu yadda mukayi iya, ba zamu iya hana Buhari karban bashi ba: Ahmad Lawan Hoto: NGRSenate
Asali: UGC

Sanatoci ba sa abinda ya kamata

Shugaban majalisar ya kara da cewa Sanatoci ba sa abinda ya kamata na bibiyan abubuwan da ma'aikatun gwamnati ke yi da kudade.

Lawan yace wajibi ne kwamitoci su tashi tsaye suyi aikinsu domin gwamnati na bukatan kudi.

"Na yarda da maganar Sanata Akpan cewa ba ma zuba ido yadda ya kamata. Ya kamata kwamitoci su san adadin kudin da ma'aikatu da hukumomi ke samu da kuma wanda suka shigarwa asusun gwamnati. Gaskiya ya kamata mu tashi tsaye.

Kara karanta wannan

Fitaccen Sanatan APC ya nuna damuwa kan yadda majalisa ke saurin amincewa Buhari ya ciyo bashi

Tattalin Arzikin Najeriya Ba Zai Samu Cigaba Ba Idan Ba Mu Ciyo Bashi Ba, Gwamnati

Ministar kudi, kasafi da tsare-tsaren kasa, Zainab Ahmed, tace cigaban tattalin arziki na kashi 5.01% da aka samu a rukunin shekara na biyu, 2021 zai samu koma baya idan ba'a ciyo bashi ba.

Ministan tace bashin da gwamnati ke ciyo wa tana zuba shi ne a ɓangaren gina muhimmman ayyukan kasa dake samar da aikin yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel