'Yan Bindiga: Matasan Arewa Sun Bayyana Matsayarsu Kan Toshe Layukan Waya

'Yan Bindiga: Matasan Arewa Sun Bayyana Matsayarsu Kan Toshe Layukan Waya

  • Wata kungiyar matasan yankin arewa ta bayyana goyon bayanta bisa toshe layukan sadarwa a wasu jihohin arewa
  • Kungiyar cikin sanarwa mai ɗauke da sa hannun shugabanta da sakatare ta ce matakin yasa sojoji na samun galaba
  • Ƙungiyar ta ce toshe layukan sadarwar ya sa ƴan bindiga ba su iya samun bayanai game da ayyukan sojojin daga ƴan leken asirinsu

Matasan arewa sun nuna goyon bayan su bisa matakin da wasu gwamnonin yankin suka ɗauka na toshe layukan sadarwa kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Gwamatin tarayya ta ɗauki matakin tsaro a jihohi kamar Zamfara, Katsina, Sokoto da Kaduna da suka hada da toshe layukan waya, hana sayar da man fetur a jarka, hana cin kasuwanni don daƙile ƴan bindigan.

Kara karanta wannan

Matsalar tsaro: Jihohin Arewa 7 sun hada kai zasu ɗauki jami'an tsaro 3,000, Masari

'Yan Bindiga: Matasan Arewa Sun Bayyana Matsayarsu Kan Toshe Layukan Waya
Layukan Sadarwa: Hoto: Daily Trust

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamnonin jihar Zamfara da Katsina sun bayyana cewa kwalliya ta fara biyan kuɗin sabulu domin sojoji na cin galaba kan ƴan bindigan a cewarsu.

Sojoji na samun galaba don 'yan bindiga ba su samun bayanai

A sanarwar da ta fitar a ranar Talata, Kungiyar Northern Youths Democratic Network ta bayyana harin da sojoji ke ƙaddamarwa kan ƴan bindiga a arewa maso yamma da maso gabas a matsayin abin da ya dace.

Sanarwar mai ɗauke da sa hannun Dauda Mathias da Yahaya Abdullahi, shugaban kungiyar da sakatare, ta ce matakin toshe layin yana taimakawa sojojin sosai.

Sanarwar ta ce matakin ya sa ƴan bindigan ba su iya sanin lokacin da sojojin za su far musu hakan yasa sojoji na samun galaba.

Masari: Muna cin nasara kan 'yan bindiga, sojoji na gasa musu aya a hannu

Kara karanta wannan

Sojoji sun hallaka kasurguman yan bindiga 5, tare da mabiyansu 23 a Zamfara

A wani labarin daban, Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina ya ce sababbin salon yaki da ta’addancin da gwamnati ta bullo da su a jihar Katsina su na aiki kuma ana samun nasarori kwarai wurin yaki da ta’addanci.

Kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito, gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Talata a wani taro wanda suka yi da ministan labarai da al’adu, Lai Mohammed akan matsalar tsaron a jihar.

Taron wanda ya samu halartar shugabannin tsaron jihar, shugabannin gargajiya, shugabannin siyasa da manyan malaman addinin da suke fadin jihar da sauran su.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel