Matsalar tsaro: Jihohin Arewa 7 sun hada kai zasu ɗauki jami'an tsaro 3,000, Masari
- Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya bayyana cewa gwamnonin jihohin arewa 7 sun amince da ɗaukar yan bijilanti 3,000
- Masari yace akwai ƙungiyoyin yan bindiga sama da 150 a cikin dazuka, waɗanda suke da shugabanni, kuma suna da alaƙa da juna
- Yace mayunwatan yan bindiga sun fara yawo ƙauyuka domin neman kayan abinci kasancewar lokacin kawo amfanin gona gida ya yi
Katsina - Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina, yace jihohi 7 a yankin arewa maso yamma da arewa ta tsakiya sun amince su ɗauki yan bijilanti 3,000 domin taimakawa wajen kawo ƙarshen matsalar tsaro.
Masari ya faɗi haka ne yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai a wurin taronsa da ministan yaɗa labarai, Lai Muhammed, da sarakunan gargajiya.
Tribune Online ta ruwaito Gwamnan na cewa rundunar yan sandan ƙasar nan ce zata horad da yan bijilantin da za'a ɗauka aiki.
Wane jihohi ne suka amince da haka?
A cewar Masari, Gwamnonin jihohin Zamfara, Sokoto, Kebbi Kaduna, Neja, Katsina da kuma Nasarawa sun gana kuma sun amince su ɗauki jami'an domin taimakawa hukumomin tsaro magance matsalar tsaro a jihohinsu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
The Cable ta rahoto Masari yace:
"A madadin gwamnonin waɗannan jihohin da na ambata, ya kamata ace sun halarci wannan taron amma ni zan wakilce su baki ɗaya."
"Ayyukan yan bindiga a arewa maso yamma da arewa ta tsakiya ya zama babbar matsala, saboda haka mun ɗauki wasu matakai don kawo ƙarshen lamarin. Akwai ƙungiyoyin yan bindiga sama da 150 a dazuka.
"Waɗannan mutanen ba su da aƙida mai kyau, addini ko wata manufa, kawai suna rayuwa ne kamar dabbobi."
Yan bindiga sun shiga halin tasku
Gwamna Masari ya ankarar cewa wasu miyagun yan bindiga sun fara yawo ƙauyuka domin satar amfanin gona yayin da ake gab da girban kayan gona.
"Saboda yunwa yan bindiga sun fara zuwa ƙauyukan dake kusa da dazuzzuka. sun san lokacin girban amfanin gona ya zo, saboda haka manufar su ita ce su saci kayan abincin da manoma suka noma."
A wani labarin na daban kuma Jam'iyyar PDP ta maidawa gwamnatin shugaba Buhari martani kan kalamanta cewa ba zata kunyata masu ɗaukar nauyin ta'addanci ba
Kakakin jam'iyyar PDP, Kola Ologbondiyan, yace wannan matakin na gwamnatin tarayya ya nuna cewa jam'iyyar APC na da alaƙa da mutanen.
Wannan dai na zuwa ne bayan haɗaɗɗiyar daular larabawa (UAE) ta aike da wasu sunayen mutum shida dake ɗaukar nauyin ayyukan ta'addanci ga gwamnatin Najeriya.
Asali: Legit.ng