Masari: Muna cin nasara kan 'yan bindiga, sojoji na gasa musu aya a hannu
- Gwamna Masari na jihar Katsina ya ce sababbin dabarun da gwamnati ta bullo dasu su na tasiri a jihar sa
- A cewar sa, yanzu haka ana ta samun nasarori masu tarin yawa sakamakon takura wa ‘yan bindiga da gwamnati ta yi
- Masari ya yi furucin nan ne a ranar Talata a wani taron da gwamnatin ta shirya don tattaunawa akan matsalar tsaro
Jihar Katsina - Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina ya ce sababbin salon yaki da ta’addancin da gwamnati ta bullo da su a jihar Katsina su na aiki kuma ana samun nasarori kwarai wurin yaki da ta’addanci.
Kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito, gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Talata a wani taro wanda suka yi da ministan labarai da al’adu, Lai Mohammed akan matsalar tsaron a jihar.
'Yan sanda za su gurfanar da wata matashiya ‘yar shekara 25 da ke yi wa ‘yan bindiga leken asiri a Katsina
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Manyan shugabannin jihar sun halarci taron
Taron wanda ya samu halartar shugabannin tsaron jihar, shugabannin gargajiya, shugabannin siyasa da manyan malaman addinin da suke fadin jihar da sauran su.
Gwamnan ya ce dakatar da kafafen sadarwa a kananun hukumomi 13 dake jihar ya haifi da mai ido saboda an datse masu ba ‘yan bindiga bayanai.
Yanzu ‘yan bindiga ba su da halin kiran jama’a don amsar kudin fansa
Kamar yadda ya ce an dakatar da masu garkuwa da mutane daga kiran ‘yan uwan wadanda suka sata don fadin kudin fansa.
Gwamnan ya ce dakatar da sayar da man fetur kusa da iyakokin jihar ma ya dakatar da yawon ‘yan bindiga daga jiha zuwa jiha.
NAN ta ruwaito yadda gwamnan ya umarci gidajen mai 2 kacal su dinga sayar wa da masu ababen hawa man fetur da ya kai N5000 a gabadaya kananun hukumomi 14 a jihar.
Masari ya hana sayar da man fetur a cikin jarkoki a gidajen mai sannan ya hana sayar da baburan da aka taba amfani da su a wasu kasuwanni.
Ya kara bayyana cewa ba zai taba sasantawa da ‘yan bindiga ba wadanda suke yaki da koyarwar addini da al’ada.
Gwamnan ya bukaci goyon bayan gwamnatin tarayya musamman wurin taimaka wa wadanda ‘yan bindiga suka cutar da kuma shugabannin addini da siyasa kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.
Tsaro: Gwamnatin Kaduna ta hana yawon gararamba da ayyukan sare itatuwa a dazukan jihar
A wani labarin daban, Gwamnatin Jihar Kana ta haramta yawon 'gararamba' a gari da shiga manyan dazuka a jihar domin yin ayyuka, The Cable ta ruwaito.
Jihar ta kuma hana sare itatuwa domin yin aikin kafinta, girki da gawayi a kananan hukumomi bakwai a jihar saboda karuwar matsalar rashin tsaro.
Kwamishinan harkokin cikin gida da tsaro na jihar Samuel Aruwan ne ya bada sanarwar a ranar Talata kamar yadda The Cable ta ruwaito.
Asali: Legit.ng