Na dauki nauyin karatunta daga Sakandare har Jami'a amma ta auri wani, Matashi ya kawo kuka

Na dauki nauyin karatunta daga Sakandare har Jami'a amma ta auri wani, Matashi ya kawo kuka

  • Wani dan kasar Ghana mai suna Richard ya nuna yadda wani yayi masa kafa a wuya
  • A bidiyon da ya daura a Facebook, ya bayyana yadda ya dauki nauyin karatun budurwarsa daga Sakandare har jami'a
  • Ya ce daga baya ya gano cewa tana tare da wani har ta aure shi da 'yaya biyu

Wani mutumi dan kasar Ghana mai suna Richard ya kawo kukan yadda budurwasa da ya dade yana kiwo daga Sakandare har jami'a amma ta auri wani mutumi daban.

A cewarsa, lokacin da ya hadu da yarinyar tana da kokarin karatu sosai amma iyayenta basu da karfin biyan kudin makaranta saboda tsananin talauci.

A bidiyon da ya daura a shafinsa na Facebook, Richard ya yi bayanin yadda yake kula da ita, yake biyan kudin makarantar har ta kammala karatu a kwalejin horar da malaman jinya.

Kara karanta wannan

Sace dalibai 73 a Zamfara: ACF ta dau zafi, ta ce duk gwamnatin da ba za ta kare al’umma ba bata da amfani

Na dauki nauyin karatunta daga Sakandare har Jami'a amma ta auri wani, Matashi ya kawo kuka
Na dauki nauyin karatunta daga Sakandare har Jami'a amma ta auri wani, Matashi ya kawo kuka Hoto:Crabbimedia
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yadda ya gano tana tare da wani

Richard ya bayyana yadda wata rana da ta ziyarce shi kuma bacci ya dibeta saboda gajiya, sai kira ya shigo wayarta da suna "Sweet Money".

Yace kasancewar tana bacci, sai ya dauki wayar tunanin cewa mahaifiyarta ce. Amma da ya daga wayar, sai yaji muryar kato yana magana cikin fushi.

Ya yanke shawarar rabuwa da ita

Richard yace daga baya kawai ya yanke shawarar rabuwa da ita saboda ransa tayi matukar baci.

Bayan lokaci kadan, sai ya gano tayi aure har da yara biyu.

Magidanta 2 Sun Bai Wa Hammata Iska Kan Budurwa, Sun Tarwatsa Motar Ɗaya

A wani labarin daban, wani turnuku fadan ibilisai ya barke tsakanin wasu maza guda biyu masu aure har suna kwankwatsa wata mota duk a kan wata mata a Makurdi, babban birnin jihar Binuwai, LIB ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Shekaru 35 yana aikin koyarwa a Borno, dan Najeriyan da Turawa suka horar ya koma talla

Kamar yadda wani Atsuwe Shadrack ya wallafa a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Facebook, inda har hotunan lalatacciyar motar ya sa, ya ce lamarin ya auku ne da safiyar Talata, 31 ga watan Augustan 2021 kusa da babbar kasuwar Makurdi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel